Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wata gidauniya mai suna ‘Khalifa Dankadai Charity Foundation’ (KDC), ta ce, ta vullo da wani shiri na ƙarfafa wa ɗaliban makarantar Ƙur’ani 6,000 da ba na boko ba a jihohi shida na ƙasar nan.
Kalmar Almajiri ta Hausa ta samo asali ne daga kalmar larabci ta ‘Al-Muhajirun’ wadda ke nufin mutumin da ya yi hijira zuwa gidansa don karatun Ƙur’ani a makarantar da ba na boko mai suna ‘Tsangaya’.
Almajiri ya kasance kalma ce ta gama-gari a arewacin Nijeriya, wanda a zahiri ana nufin matashin da ke bara a kan tituna kuma ba ya zuwa makarantar boko.
Jami’in kula da ayyukan na gidauniyar, Khalifa Dankadai ne ya bayyana hakan a lokacin buɗa baki da masu ruwa da tsaki a harkar zamantakewa a daren Litinin a Kano.
Ya ce, an tsara tsarin karatun ne domin gyara tsarin makarantar Tsangaya a jihohin Katsina, Kano, Neja, Jigawa, Zamfara da Sakkwato.
Dankadai ya ƙara da cewa, za a gudanar da shirin ne a wasu zaɓaɓɓun makarantu 60 da ke faɗin yankin, inda ya ce, ɗalibai 1,000 ne za su ci gajiyar shirin a kowace jihohin da za a shiga.
Dankadai ya ce, haɗakar masu ruwa da tsakin ita ce yin mu’amala da masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta, da kuma tsara hanyoyin da za a inganta harkar wayar da kan jama’a domin hanzarta bin diddigin gyara tsarin karatun Almajiri.
A nasa jawabin, Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa na zamani da sabbin kafafen yaɗa labarai, ya yaba da wannan karimcin tare da yin alƙawarin tallafa wa gidauniyar domin samun damar cimma manufofinta.
A nasa ɓangaren, Sha’aban (APC – Kano Municipal Federal Constituency) ya jaddada ƙudirin majalisar dokokin ƙasar na samar da sahihin dokoki domin sauƙaƙa wa tsarin makarantar Tsangaya garambawul.
Sharada, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, ya jaddada ƙudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.