Gidauniyar Muktariyya ta yi bikin yaye ɗalibai a Kano

Daga HARUNA AKARAɗA a Kano

Gidauniyar Mukhtariyya ta gudanar da bikin yaye ɗalibai karo na biyar a Jihar Kano.

Jigo a Jam’iyyar APC ta Jihar Kano, Hon Dr. Mukhtar Ishaƙ Yakasai (Jagora), kuma shugaban cibiyar gidauniyar Mukhtariyya, shine yake ɗaukar nauyin karatun ɗaliban kyauta, domin cigaba tallafawa mara ƙarfi da marayu a Jihar Kano.

Wannan taro ya samu  halartar manyan baƙi na jam’iyyar APC dake Jihar Kano kamar su tsohon kwamishinan ilimi, Hon. Sanusi Sa’id Kiru, tsohowar kwamishiniyar mata, Malama Dr. Zahara’u, tsohon kwamishinan addini, Dr. Muhammad Nafizi Bichi, Hon, Ahmad S Aruwa, S A.Alhaji Tijjani Mailafiya Sanka, Shugaban gamayyar matasan Jam’iyyar APC na jihar Kano.

Sauran sun haɗa da Hon. S.A Adam Mukhtar Unguwar Gini E.S Yahaya Garin Ali, ɗan Maliki Dr Auwal Mudi Yakasai, Wakilin Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi, E.S Alhaji Sale Jili, Wakilan DG Alhaji Uba Danzainab, Hon. Isyaku Gambaga, tsofaffin mataimaka na musamman, tsofaffin chiyamomi da kansiloli da muhimman mutane sun sami halarchi taron

An gudanar taron a babbar tiyata ta Mahmoud Tukur dake tsohuwar Jami’ar Bayero dake jihar Kano bayan kammala taron yaye ɗaliban mun samu tattaunawa da Honarabul Alasan Ado Doguwa dangane da irin wannan gudunmawa da Honarabul Muntari Ishaƙ Yakasai yake kawowa jihar Kano,  lallai shi kansa ya ɗauki darasi kan wannan  zai koyi da haka. 

Tsohon Kwamashinan ilimi Hon. Sanusi Sa’id Kiru ya ce wannan abinda Muntari Ishaƙ ya yi shi abin koyi nagari.   

Shi kuwa Honarabul Muntari Ishaƙ Yakasai ya gode wa duk waɗanda suka zo wannan taron ya ce dalilin yin wannan aikin na tallafin ɗalibai nan ya ce ya lura dukkaninsu yaran basu da ƙarfin iya biyan komai a rasuwarsu, yace shi ne karo na biyar.