Gidauniyar Sadiq Maira da haɗin kan hukumomi mu ke yaƙi da cin zarafin yara – Sayyada Umaira

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Shugabar Gidauniyar Sadiq Maira, Ambasada Sayyada Umaira Sadiq, Tauraruwar Hausawan Afirka ta ce gidauniyar su ta Sadiq Maira Foundation for the Less Privileged, tana yaƙi da cin zarafin ‘ya’ya mata da kuma taimaka wa marasa galihu.

Ambasada Sayyada Umaira, ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da wakilin mu, a Gombe, inda ta ce suna haɗa kai da jami’an tsaro da alƙalan kotuna har ma da hukumomi wajen ƙwato wa duk wata yarinya da aka yi wa fyaɗe ko aka ci zarafin ta ‘yanci.

Ta ce idan suka samu rahoton cin zarafi ko fyaɗe sai inda ƙarfin su ya kare wajen tsayawa wacce aka lalatawa Rayuwa kuma idan suka kai lamarin Kotu suna samun nasara.

Sayyada Umaira, ta yi amfani da wannan damar ta yi kira ga iyaye da suke ɓoye ‘ya’yan su da aka ci wa zarafi da cewa boyewan ba alheri bane su dinga bayyanawa don bi musu kadun su don ganin an hukunta wanda ya aikata laifin don ya zama izna ga masu sha’awar aikata hakan nan gaba.

Tauraruwar Hausawan Afirka, ta gode wa wasu gwamnonin jihohi musamman jihar Gombe da Yobe da suka sa hannu kan dokar hana cin zarafin yara, wanda take nuni da cewa duk wanda aka kama zai gamu da fushin hukuma.

A cewarta a ƙarƙashin gidauniyar ta sun tallafa wa marayu da marasa galihu da yawa sun koyawa wasu ma sana’o’in hannu daban-daban don dogaro da kan su.

Sannan ta ce tana mai goyon bayan ɗaukar matakin da ya dace kan kowanne lalataccen namiji da aka kama shi da yi wa yara fyaɗe ko cin zarafinsu.

Daga nan sai ta kara gode wa alƙalai da jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen tsayawa bil haqqi da gaskiya suke kare ‘yancin duk wanda aka zalunta da suka kai musu.