Ginin Hedikwatar ECOWAS: Al’ummar Afrika ba za su taɓa mantawa da tallafin ƙasar Sin ba

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Tasiri da taimakon kasar Sin ga nahiyar Afrika kawo yanzu, abubuwa ne da ba za su iya misaltuwa ko bayyanuwa ba, saboda yawansu da kuma karfi da moriyar da suke samarwa.

A farkon makon nan ne aka aza tubalin ginin hedkwatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Inda ya kasance wani katafaren aiki, kuma babbar nasara ga kungiyar ta ECOWAS, domin a karon farko, muhimman sassanta uku, wato kotun kungiyar da majalisar dokoki da sakatariyarta, za su kasance a dunkule, karkashin inuwa guda maimakon yadda suke a mabambantan wurare.

Hakika, taimakon kasar Sin na gudanar da wannan aiki tare ma da samar da kudin aiwatar da shi, ya nuna yadda ta damu da ayyukan kungiyar, kuma take fatan ganin nasarori da ci gabansu da ma hadin kansu wajen tunkarar kalubalen dake gabansu, bisa la’akari da yadda kasancewar sassan kungiyar a dunkule, zai rage kudin da ake kashewa tare da kara kaimi kan ayyukan da ake gudanarwa.

Kamar yadda jakadan na Sin a Nijeriya Cui Jianchun ya bayyana, ginin zai taka rawa wajen fadada dangantakar Sin da kasashen yammacin Afrika.

A ganinsa, ba kyautata dangantakar Sin da kasashen zai yi ba kadai, har ma tsakanin kasashen kungiyar da kansu a wannan zamani da ake fuskantar dimbin klalubale. Baya ga haka, ya nuna yakinin da Sin ke da shi wajen ganin an samu hadin kai a tsakanin kasashen da ma karfin shawo kan matsalolin dake addabarsu.

Idan muka dubi mai masaukin baki wato Nijeriya da ta bayar da filin ginin, za mu gano cewa, ba kungiyar ECOWAS kadai ce za ta amfana da wannan alheri na kasar Sin ba, domin Nijeriya sai ta fi kowa cin moriya. Kamar yadda hedkwatar kungiyar tarayyar AU da Sin ta gina a Addis Ababa, ya kasance babba, kuma muhimmiyar alama, haka wannan gini ma zai zama wata babbar alama a bangaren gine-gine da kawata birnin Abuja.

Haka zalika, tsawon lokacin aikin, zai bunkasa tattalin arzikin yankin da ma birnin, domin zai bude wata kasuwar hada-hada a kowanne bangare na kasuwanci.

Har ila yau, zai samar da dimbin guraben ayyukan yi, wanda a ganina, za su rage zaman kashe wando tsakanin matasa da aikata miyagun ayyuka.

Bugu da kari, fasahohin da Sin za ta yi amfani da su, zai kara ba Nijeriya gogewa da karin ilimi kan dabaru da fasahohin gine-gine na kasar Sin.

Kamar a ko da yaushe, kasar Sin ta cancanci yabo domin tana kara nuna matsayinta na babbar kasar da ta san ya kamata, kuma aminiya ta kwarai dake da burin ganin ci gaban kawayenta, kuma abun dogaro gare su.

Hakika, al’ummar Nijeriya da ma Afrika, ba za su taba mantawa da alherin kasar Sin ba.