Girgizar ƙasa ta kashe mutum 268 a Indonesiya

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga ƙasar Indonesia sun ce aƙalla mutum 268 ne suka mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a tsibirin Java da ke ƙasar.

Bayanai sun ce iftila’in ya rutsa har da ɗaliban makaranta.

Girgizar ƙasar wadda ta auku ranar Litinin da ta gabata, ta kai ƙarfin maki 5.6 ta yi sanadiyyar lalacewar gidaje da daman gaske a yankin.

Kazalika, hatsarin ya jikkata mutum 700 tare da lalata ɗimbin dukiya kamar yadda hukumomin ƙasar suka bayyana.

Masana sun ce yanayin ƙasar ya sa ake yawan samun aukuwar girgizar ƙasa a Indonesia.