Daga BASHIR ISAH
Rahotanni daga ƙasar Moroko sun ce, sama da mutum 296 sun mutu sakamakon girgizar ƙasa mai karfin maginitud 6.8 da ya auku a ƙasar.
Jami’ai sun ce galibin waɗanda suka mutu mutanen da suka maƙale ne a ɓuraguzan gine-gine wanda kai wa gare ya yi wahala balle a cece su a yankunan Kudancin Marrakech.
Iftilain girgizar ƙasar ya auku ne da sanyin safiyar wannan Asabar ɗin, lamarin da ya haifar da zubewar gine-gine a wasu manyan biranen ƙasar.
A ƙalla mutum 153 aka rawaito sun jikkata kuma ana yi musu magani a asibiti.
An ga jami’ai a yankin suna aiki wajen share hanya don bai wa motocin jigilar marasa lafiya zirga-zirgar aikin ceto a yankin.