Girgizar ƙasar Siriya-Turkiyya: Yawan matattu ya kai 5000, gidaje 5775 sun rushe

Daga BASHIR ISAH

Kawo yanzu, kimanin mutum 5,000 aka tabbatar sun mutu, wasu dubbai sun jikkata a girgizar ƙasar da ta auku a Turkiyya da Siriya a ranar Litinin.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Mataimakin Shugaban Ƙasar Turkiyya, Fuat Oktay, da safiyar ranar Talata.

Ya ce mutum 3,419 sun mutu yayin da 20,534 sun jikkata a Turkiyya.

A ɓangaren Siriya kuwa, yawan waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 1,602, wanda baki ɗaya jimillar ta kama 5,021.

Hukumar kula da iftila’i ta ƙasar Turkiyya, ta ce rahotanni sun nuna gidaje 11,342 girgizar ta shafa, amma gidaje 5,775 ne aka tabbatar da rushewarsu.

Masu aikin ceto sun ce suna fama da ƙarancin wasu kayan aikin da za su taimaka musu wajen zaƙulo waɗanda suka maƙale a ɓuraguzan gine-ginen da suka rushe da sauransu.

An ce wannan ita ce girgizar ƙasa mafi munin da Turkiyya ta gani sama da shekaru 100.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *