Girgizar ƙasar Turkiyya: An gano gawar Christian Atsu

Daga BASHIR ISAH

An gano gawar tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Ghana, Christian Atsu, wanda girgizar ƙasa ta rutsa da shi a Turkiyya.

Kafar yaɗa labarai ta Turkiyya ta rawaito cewa, an gano gawar ɗan wasan ne ranar Asabar a ƙarƙashin ɓuraguzan ginin da ya rushe kamar yadda manajansa ya bayyana.

Da fari rahotanni sun nuna an ceto marigayin kwana ɗaya da aukuwar iftila’in, amma a ƙarshe ya zamana ba gaskiya ba ne.

Sai a ranar Asabar manajan marigayin a Turkiyya, Murat Uzunmehmet, ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta DHA cewar an gano gawar marigayin a ƙarƙashin ɓuraguzan ginin da ya rushe sakamakon girgizar ƙasar.

“Mun gano gawarsa, ana ci gaba da binciko sauran kayayyakinsa. Haka ma an gano wayarsa,” in ji Uzunmehmet ga kafar DHA.

Ita ma tsohuwar kulob ɗin marigayin, Newcastle United, ta tabbatar da mutuwar marigayin da safiyar Asabar.