Gobara ta ƙone shaguna 41 a Kasuwar Kurmi da ke Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da ƙonewar shaguna 41 a ɓangaren ƴan Littafi da ke ƙasuwar kurmi a ƙaramar hukumar birni ta jihar Kano,

Saminu Abdullahi, wanda shi ne Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar ne ya tabbatar da gobarar a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a yau Litinin.

Abdullahi ya ce hukumar ta ƙarɓi rahoton gobarar ne ta wayar salula daga wani Malam Bala Nasidi da misalin ƙarfe 10:58 cewa akwai gobara a ƴan littattafai kasuwar.

“Muna karɓar rahoton, bamu yi ƙasa a gwiwa ba mu ka garzaya wajen da misalin ƙarfe 2:07 na safe domin kashe wutar.

Abdullahi ya tabbatar da cewa ƙananan rumfuna ne 37 su ka ƙone, sai kuma ginannun shaguna guda 4 da su basu ƙone ƙurmus ba sakamakon kai ɗauki da dakarun hukumar su ka yi.

Ya yi bayanin cewa tartsatsin wutar lantarki ne ya haifar da gobarar.

Ya kuma yi kira da ƴan kasuwa da su tabbatar sun kashe duk wasu kayan lantarki da mukunnan wuta a lokacin tashi daga kasuwa.