Gobara ta ƙone shaguna da dama a Kwara

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga Jihar Kwara sun ce shaguna da dama sun ƙone tare da asarar dukiya mai yawa sakamakon ƙobarar da ta auku a Kasuwar Owode da ke garin Offa a jihar.

An ce gobarar ta fara ne da asubahin Talata wanda hakan ya yi sanadiyar ƙonewar wasu shaguna a kasuwar.

Cikin wani faifan bidiyo na gobara wanda aka yaɗa an jiyo murya cikin harshen Yarabanci na cewa: “Wutar ta yi ƙarfi sosai, ba lantarki ya haifar da gobarar ba, wataƙila sakamakon girki da ake yi kusa da wurin ne.”

Bayanai sun daga bisani, Jami’an Kwana-kwana na ji da Tarayya sun samu nasarar kashe gobarar.

Ya zuwa kammala wannan rahoto, babu wani bayani kan adadin ɓarnar da gobarar ta yi a kasuwar.