Gobara ta laƙume rumfunan kasuwa 80 a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta rawaito cewa, gobara ta lamushe aƙalla rumfuna 80 a kasuwar Kurmi da ke cikin ƙwaryar birnin Kano. 

Wannna jawabi ya fito ne daga bakin kakakin hukumar kashe gobara a Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, a ƙarfe 5:23 ranar Larabar da ta gabata. 

Abdullahi ya bayyana cewa, sun samu waya ta neman agaji daga wani wai shi  Aliyu Alkasim wanda ya gaya musu cewa gobara ta varke a kasuwar. 

Ita dai kasuwar Kurmi kasuwa ce a Kano wacce ta shahara a sayar da kayan ƙamshi, turare, da fatun dabbobi. 

Kakakin ya bayyana cewa, manyan rumfuna guda 6 ne suka ƙone yayin da rumfunan wucin-gadi guda 74 ne suka ƙone ƙurmus. 

Haka zalika, Abdullahi, ya tabbatar da cewa ba a rasa rainko ɗaya ba, kuma ba wanda ya jikkata a sakamakon gobarar. Kuma ya ƙara da cewar, suna nan suna binciken musabbabin gobarar. 

Daga ƙarshe, Abdullahi ya shawarci ‘yan kasuwa su dinga kashe kayan lantarki a kasuwa idan an tashi, sannan a yi taka-tsan-tsan wajen amfani da tsurar wuta musamman a farfajiyar kasuwa.