Daga AMINA YUSUF ALI
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta rawaito cewa, gobara ta lamushe aƙalla rumfuna 80 a kasuwar Kurmi da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.
Wannna jawabi ya fito ne daga bakin kakakin hukumar kashe gobara a Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, a ƙarfe 5:23 ranar Larabar da ta gabata.
Abdullahi ya bayyana cewa, sun samu waya ta neman agaji daga wani wai shi Aliyu Alkasim wanda ya gaya musu cewa gobara ta varke a kasuwar.
Ita dai kasuwar Kurmi kasuwa ce a Kano wacce ta shahara a sayar da kayan ƙamshi, turare, da fatun dabbobi.
Kakakin ya bayyana cewa, manyan rumfuna guda 6 ne suka ƙone yayin da rumfunan wucin-gadi guda 74 ne suka ƙone ƙurmus.
Haka zalika, Abdullahi, ya tabbatar da cewa ba a rasa rainko ɗaya ba, kuma ba wanda ya jikkata a sakamakon gobarar. Kuma ya ƙara da cewar, suna nan suna binciken musabbabin gobarar.
Daga ƙarshe, Abdullahi ya shawarci ‘yan kasuwa su dinga kashe kayan lantarki a kasuwa idan an tashi, sannan a yi taka-tsan-tsan wajen amfani da tsurar wuta musamman a farfajiyar kasuwa.