Gobara ta tashi a Kasuwar Singa dake Kano

Daga WAKILINMU

Bayanai daga Kano sun tabbatar da aukuwar gobara a fitacciyar kasuwar nan ta Kano, wato Kasuwar Singa.

Majiyarmu ta ce gobarar ta fara ne da tsakar daren da ya gabata zuwa safiyar Litinin.

An ga jami’an kwana-kwana tare da ‘yan kasuwar a lokacin da suke ƙoƙarin kashe gobarar wadda ta ƙone shaguna da daman gaske.

Abubakar Aminu, na ɗaya daga cikin ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa, ya shaida wa jaridar News Point cewa ya samu kiran waya da misalin ƙarfe 1:15 na dare, kuma da ya isa kasuwar da misalin ƙarfe 2:00 na daren, ya tarar da shagonsa na ci da wuta ta yadda babu yadda za a iya shiga a ɗauki wani abu.

Ya ƙara da cewa, gobarar ta ƙone shaguna sama da 100 a kasuwar tare da lalata kayayyaki na miliyoyin Naira.

“Gaskiya mun tafka asara babba. Jiya-jiya ɗin nan aka sauke wa maƙwabcina kaya tirela uku, gobarar ta ƙone kayan baki ɗaya,” in ji shi.

Kasuwar Singa na nan ne a hanyar Ibrahim Taiwo a birnin Kano, kuma ita ce kasuwar abinci mafi girma da shahara a jihar.

Ga ƙarin hotunan iftila’in: