Gwamnatin Tarayya ta umarci a gaggauta ɗaukar dukkan mutanen da suka jikkata a gobarar fashewar tankar mai da ta faru a Suleja, Jihar Neja, zuwa manyan asibitocin koyarwa domin samun kulawa ta musamman. Ministan bayani da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana haka yayin ziyarar da ya kai Suleja tare da wata babbar tawaga ta gwamnati domin jajanta wa al’ummar jihar da kuma duba halin da ake ciki.
Ministan ya bayyana jimamin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu game da mummunan lamarin da ya faru a Dikko Junction, Suleja. Ya ce: “Shugaban Ƙasa yana cikin matsanancin baƙin ciki kan wannan al’amari. Ya umurce mu mu zo mu duba halin da ake ciki. Mun ziyarci waɗanda suka jikkata sosai kuma a lokacin da muke ziyara, wani daga cikinsu ya rasu, wanda ya kasance mutum na takwas da ya rasa ransa tun bayan fashewar. Yanzu haka gwamnatin tarayya na ƙoƙarin kwashe su zuwa manyan asibitoci domin samun kulawa ta gaggawa.”
Ya kuma yabawa gwamnatin Jihar Neja kan saurin da ta ɗauka wajen samar da taimakon gaggawa ga waɗanda abin ya shafa. Ministan ya bayyana damuwa kan adadin rayukan da aka rasa sakamakon fashewar tankar mai, wanda ya kai kimanin mutane 265 a cikin watanni biyar da suka gabata. Ya ce shugaban ƙasa ya kafa kwamiti domin binciko dalilan faruwar irin waɗannan haɗurra da kuma samar da mafita mai ɗorewa.
A cewar Ministan, gwamnatin tarayya za ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a game da illolin tattara man fetur daga motocin da suka yi haɗari, ta hanyar hukumar wayar da kan jama’a (NOA). Ministan ya jaddada cewa irin wannan ɗabi ’a na tattara mai ba daidai ba ne kuma gwamnati ba za ta amince da shi ba. Tawagar gwamnatin tarayya ta kuma kai ziyara ga Sarkin Suleja, Alhaji Auwal Ibrahim, da waɗanda suka jikkata a asibitin Suleja, tare da duba wurin da abin ya faru.