Gobarar tankar gas ta yi sanadin ƙone motoci da shaguna a Neja

Daga BELLO A. BABAJI

An sake samun wani hatsarin gobara a Jihar Neja bayan da wani abin fashewa ya tarwatse a yankin Sabon-Wuse na ƙaramar hukumar Tafa, wanda ya yi sanadiyyar ƙone wasu motoci da shaguna.

Darakta-Janar na Hukumar Bada Agajin Gaggawa a jihar (NSEMA), Abdullahi Baba-Arah ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi inda ya ce ba a samu asarar rayuka ba.

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Asabar, a lokacin da wata tanka ta ke sauke gas a wani gidan mai.

Shaidu sun bayyana cewa al’amarin ya sanya al’umma cikin fargaba kasancewar nan take wutar gobarar ta yaɗu zuwa wani wajen man fetur tare da lanƙwame shaguna da wasu kadarorin al’umma.

Jami’an kashe gobara sun halarci wajen da abin ya faru bayan sa’o’i da faruwarsa.

Tuni dai mazauna yankin suka buƙaci hukumomi da su samar da dokokin kulawa ga gidajen gas da fetur don ƙaurace wa faruwar irin haka a nan gaba.