Gobe Asabar za a ƙaddamar da littafi kan fyaɗe a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gobe Asabar ne dai za a ƙaddamar da littafin fyaɗe mai suna ‘Fyaɗe Makamin Cutar da Al’umma’,  wanda Falalu Yunusa Abubakar ya rubuta, wanda malami ne a Hukumar Makarantun Sakandire ta Jihar Kano (KSSSMB).

Malamin, ya rubuta littafin ne dai dangane da illoli da matsalolin da fyaɗe ke haifarwa a cikin al’umma.

A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ƙaddamar da littafin, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya rabawa manema labarai a Kano, ya ce za a ƙaddamar da littafin ne a a gidan Mumbayya da ke Gwammaja a cikin birnin Kano.

Sanarwar ta ci gaba da cewa babban mai ƙaddamarwa shi ne sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Barau I. Jibrin (Maliya), sai babbar baƙuwa ta musamman Hajiya Salamatu Garba (WOFAN), sai mai sharhi littafin shahararriyar ‘yan jarida Hajiya Halima Bin Umar, wanda uban taro zai kasance Hakimin Tsanyawa Alh. Mu’awiya Abbas Sunusi. Yayin da shugaban taro zai kasance Farfesa Yusuf Adamu.

Za dai a yi taron qaddamarwar ne a ɗakin taro na Sa’adu Zungur da ke Gwammaja cikin birnin Kano da ƙarfe 10:00 na safe.