Gobe Barno za ta karɓi baƙuncin Buhari

Daga AMINA YUSUF ALI

Ana sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a jihar Barno ran Alhamis idan Allah ya kai mu.

Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, shi ne ya bayyana haka yayin jawabin da ya yi wa ‘yan jihar kai tsaye a kafar yaɗa labarai a Maiduguri. Tare da kira ga talakawansa da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata domin tarbar babban baƙon nasu.

A cewar Zulum Buhari da tawagarsa za su ziryaci Barno ne domin la’akari da sha’anin tsaro na yankin Arewa-maso-gabas, kana ya ƙaddamar da tarin ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar a tsakanin shekaru biyu da suka gabata.

Yayin da ya yi godiya ga talakawansa dangane da irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa, Zulum ya yi kira ga al’ummar jihar da su zamana masu bin doka da oda kafin da yayin da kuma bayan ziyarar shugaban ƙasar.

Yayin jawabin nasa, Zulum ya shaida wa ‘yan jiharsa cewa, “Da yardar Allah Shugaban Ƙasa zai ziyarci Maiduguri ranar Alhamis 17 ga Yuni, 2021, musamman don duba sha’anin tsaro a yankin Arewa-maso-gabas, sannan zai ƙaddamar da wasu ayyukan cigaban jihar da gwamnati ta aiwatar.