Gobe Masarautar Gaya za ta yi bikin naɗa Sheikh Yusuf Ali Sarkin Malaman Gaya

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Gobe Asabar Masarautar Gaya za ta yi bikin naɗin Sarauta wanda a ciki za ta naɗa Sheikh (Imam Dr.) Yusuf Ali a matsayin Sarkin Malaman Gaya.

Bikin naɗin ya biyo bayan sahalewar Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji (Dr) Ibrahim Abdulƙadir (Kirmau Mai Gabas) ne. Sarautar Sarkin Malamai sarauta ce da ta shafi dukkan al’amuran addini na masarauta.

A Sanarwar da masarautar ta fitar a ranar talata 13 ga Yuli, 2021, ta amince da ranar Asabar 17 ga Yuli, 2021, ta zama ranar naɗin.

Idan ba a manta ba, a ranar 17 ga watan Agustan bara, 2020, Mai Mai Martaba Sarkin Gaya ya aika da takardar amincewa da naɗa Sheikh Yusuf Ali a matsayin Sarkin Malamai, takardar da Sakataren Masarautar, Marigayi Shazali Adamu Gaya, ya sa wa hannu.

A takardar Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Dr Ibrahim Abdulƙadir, ya ce, “wannan naɗin an yi shi ne, saboda cancantarsa da gaskiyarsa da riƙon amanarsa da gogewarsa wajen tafiyar da al’amuran jama’a da kuma kishin wannan masarauta da ya ke da shi.”

Za a yi wannan gagarumin biki ne a na wannan naɗin a babbar fadar Gaya a cikin garin Gaya da misalin ƙarfe 11 na safe idan Allah ya kai mu.