Gobe za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH

Gobe Laraba ake sa ran gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Nasarawa inda jama’a za su fito su zaɓi ciyamomi da kansilolin da za su ci gaba da jan ragamar ƙananan hukumomin nan da shekaru uku masu zuwa.

Kafin wannan lokaci an ga ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban sun ba da himma wajen yaƙin neman ƙuri’un jama’a yayin zaɓen na gobe.

Ana sa ran gudanar da zaɓen ne a baki ɗayan ƙananan hukumomi 13 da ake da su a faɗin jihar.

Gwamna Abdullahi Sule

Da yake bayani a wajen wani taronsu na siyasa kwanan nan a garin Akwanga, Gwamnan Jihar, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce gwamnatin jihar ta shirya ma wannan zaɓe yadda ya kamata.

Tare da cewa, ana sa ran zaɓen ya gudana cikin salama ba tare da tada wata ƙura ba, sannan a ƙarshe, duk wanda ya ci zaɓe a miƙa masa kayansa kamar yadda dokar zaɓen jihar ta tanadar.