Gombe a 2023: Inuwa da Goje sun fara sa zare

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Rikicin cikin gida ya kunno kai, wanda ya ke neman raba kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a Jihar Gombe, inda aka fara takun saƙa tsakanin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da magoya bayansa da kuma tsohon ubangindansu a siyasa kuma tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Muhammad Danjuma Goje, wanda shine sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya a halin yanzu.

Rikicin ya fara kunno kai ne a lokacin da jam’iyyar ta shirya zaɓen shugabanni na matakin gunduma a dukkan faɗin ƙasa, inda shi Sanata Goje ake ganin ya so yin abin da ya so a yankinsa ta hanyar zaɓen waɗanda ya so su koma kan kujerarsu a tsarin shugabancin jam’iyyar, ya kuma canja waɗanda ba sa tare shi, inda hakan ya sa aka ji gwamnan ya fito a bainar jama’a yana nuna jin daɗinsa, yana mai faɗin cewa, shi bai yarda ba, saboda babu wanda zai yi masa kama-karya yana matsayin gwamna, domin sanata bai fi gwamna ba, sannan daga nan ake ganin gwamnan ya ɗauki matakan daƙilewa da rage ƙarfin ikon sanatan a cikin jam’iyyar.

Hakan ta sanya wasu mabiyan Sanata Goje suka riƙa ajiye muƙamansu na jam’iyya, su na haƙura kacokam, saboda cin zarafin maigidansu da suka ce a ke yi. Wannan ya sa mutane suke ganin kamar gwamnan ya ɗebo abin da zai ja masa matsala, saboda suna ganin kamar faɗa da ya ke yi da ubangidansa, Goje, zai iya sawa ya rasa kujerarsa ta gwamna a shekarar 2023, domin da ma faɗan a ɓoye ya ke, amma yanzu ya fito fili.

Wannan al’amari ya sa a ranar Lahadin da ta gabata masu ruwa da tsaki da jiga-jigan ’yan siyasar yankunan mazaɓar sanatan na Gombe ta Tsakiya, wato ƙananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba, suka taru a garin Deba suka gudanar da taro kan nuna goyon bayansu ga Gwamna Inuwa Yahaya da suke cewa, shi ne jagoransu, ba sanata Danjuma Goje ba.

Da ya ke jawabi a wajen wannan taron, ɗan Majalisar wakilai ta Tarayya mai wakiltar Akko, Hon. Usman Bello Kumo, cewa ya yi, su ba sa tare da Danjuma Goje, domin siyasa ba gado ba ce; su jagoransu a siyasa a yanzu kuma ubangidan su shine  Gwamna Muhammad Inuwa, kuma duk wanda ba zai bi shi ba, sai dai ya bar jam’iyyar.
Usman Kumo ya ce, “ai ko jihohin da suke da ’ya’yansu a manyan muƙamai, suna ƙarƙashin gwamnansu ne. Me ya sa a Gombe wani zai riƙa jin cewa, shine jagora, ba gwamna ba?”

Ya bada misalai da wasu jihohi, inda cikinsu har da Jihar Yobe da suke da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, wanda shine mutum na uku a Najeriya, amma Gwamnan Jihar, Alhaji Mai Mala Buni, ne jagoransa. Ya cigaba da cewa, bai ga dalilin zai sa da wani zai ce, idan ba shi ba, babu wanda ya iya ba.

Shi ma tsohon sanata kuma tsohon Ministan Sufuri da ake ganin yana daga cikin waɗanda suke sansana kujerar sanata da Goje ya ke kai, Barista Idris Abdullahi Umar, cewa ya yi, manufarsu ta shirya wannan taro ita ce, su dunƙule waje ɗaya, su ƙara wa APC ƙarfi a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya.

Ya ƙara da cewa, duk wani zaɓe da ake yi, su ’yan Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ne suke kawo ƙuri’a mafi rinjaye bayan Gombe. Don haka suka ga cancantar ƙara mara wa Inuwa Yahaya baya, don ya sake dawo wa karo na biyu, yana mai cewa, manufarsu kuma ta cika.

A jawbainsa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Rt. Hon. Abubakar Luggerewo, cewa ya yi, cancantar da gwamna ya yi bisa ayyukan raya ƙasa da ya ke yi shi ya sa su a majalisa su suka jefa masa ƙuri’ar amincewa ya ci gaba har zuwa shekarar 2027.

Jigo a jam’iyyar kuma jagoran wannan taron, Alhaji Abubakar Habu Mu’azu, ya bayyana cewa, wasu na cewa, “Gwamna Inuwa Yahaya ya ci amanar Danjuma Goje, ya fara faɗa da shi. Ba haka ba ne. Goje bai kyauta ba, kuma dole a nuna masa rashin kyautawar da ya yi. Saboda biyayyar Inuwa Yahaya da ya ke yi wa Goje, ya bai wa ’yarsa da surukinsa da wasu aminansa muƙaman kwamishoni. Ashe idan haka ne kuwa Inuwa Yahaya bai ci mutunci ko saɓa wa Goje ba.”

Yanzu dai abun jira a gani shine, ya waƙar za ta ƙare, domin wasu na hasashen cewa, jam’iyyar na shirin korar Sanata Danjuma Goje daga cikinta kuma kujerar tasa shi kansa ɗan majalisar mai wakiltar Akko, Hon. Kumo da Barista Idris ɗin da ma Alhji Mu’azu ɗin, su na yin harinta; shi ya sa ake faɗan. Amma idan ma sun kore shi, shin a cikinsu ukun wa zai haƙura ya bar wa wani a jam’iyyar? Lokaci ne kaɗai zai tabbatar da hakan.

To, sai dai kuma a ɓangaren mabiyan Sanata Danjuma Goje da suka ajiye muƙamansu, Sale Muhammad, wanda aka fi sani da Sale Gudduri 5 Deligate a Akko, ya ce, sun ajiye muƙaman ne saboda ba a sanya maigidansu a cikin tsarin zaɓen shugabannin gundumomin ba a jam’iyyar tasu ta APC, wanda hakan rashin girmamawa ne gare shi, idan aka yi la’akari da matsayinsa a siyasar jihar da kuma jam’iyya mai mulki.

Ita ma Shugabar Mata ta Kumo ta Tsakiya, Zainab Musa Idi, mai inkiya da Anti Zee, ta ce, ta ajiye muƙamin ne ba don kawai saboda tana da alaƙa mai ƙarfi da Sanata Goje ba, amma sai yadda aka yi masa wajen rashin sa shi a tafiyar da zaɓen shugabannin ya sa suke ganin ba a kyauta masa.

Inuwa da Goje

Amma a ɓangaren magoya bayan Gwamnan Inuwa Yahaya kuma Alhaji Salihu Jarman Kumo cewa ya yi, tun farko ne ba a bi cancanta ba wajen zaɓen har aka zaɓo marasa kishin jam’iyyar da suke amsa kiran wani wanda duk lokacin da ya ce su ajiye saboda kwaɗayi za su ajiye. Sai dai kuma wasu na ganin cewa, ai idan don kwaɗayi ne, gwamnati za a fi bi.

Amma Jarman Kumo ya ce, duk kururuwar da ake yi na cewa, wasu sun ajiye muƙaman nasu, babu mutum 10 da suka ajiye, kuma a kowacce gunduma suna da mutum 27, suna da kwamiti na mutum 25 a matakin ƙananan hukumomi 25 a matakin jiha, kuma bayan ajiyewar tasu an samu mutune fiye da 100 suna jiran a ba su muƙaman.