Gudun a kira ni da kalmar bazawara ya sa nake haƙuri da duka da musgunawar da mijina ke yi min

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Salam. Asas barka da wuni. Ya aiki da kuma iyali. Sannu da ƙoƙarin ba wa mata shawarwari da ki ke yi. Allah ne kawai mai iya saka mi ki kan taimakon da ki ke yi. Allah Ya sa aljanna ce sakamakon, amin. Don Allah ki ba ni shawara. Mijina ne ban taɓa jin daɗin zama da shi ba. Yau shekara 14 cikin ta 15 da aure, amma ba wani alherinsa da zan iya tunawa ga rayuwata.

Tun wata biyu bayan aurenmu ya fara duka na, matsalar abinci tun lokacin na fara samun ta, saboda ma na ce babu shinkafa ne ma ya yi min dukan a ranar. Duka, rashin abinci, neman matan banza da rashin fita su ne halayar da yake min. A haka na haifi yara uku, amma har yau bai canza ba, sai ma abinda ya ƙaru, don sati biyu da suka wuce duka ya yi min har sai da na suma, yarona ne ma ya kira maƙwabciyar mu ta taimaka min.

Wallahi Ina shan matuƙar wuya wurin sa, kuma kullum lamarin sai ƙaruwa yake. Idan na tuna wahalar da na ke sha sai inji kamar in haƙura da auren, gudun a kira ni da kalmar bazawara ne ke taka min birki. Kin dai san yadda ake kallon zawarawa tare da aibata su. Ki taimaka min da yadda zan magance matsalata don Allah. Ko laƙani ne da zai hana shi duka na, ko ta nan in samu sasauci.

AMSA:

A vangaren ciyarwa, yana ɗaya daga cikin wajibban da ake kallo kafin a ce ka isa yin aure, ma’ana duk namijin da baida abin ciyar da iyali, to bai kamata ya jajubo aure ba. Muhimmancin ciyarwa ne ya sa aka ce, ku auri matan da suke daidai ku, ma’ana bai kamata ka auri macen da ba ka iya bata koda kashi hamsin na irin rayuwar da ta saba da ita a gidansu ba, saboda me, muhimmancin ciyarwa da yadda yake iya kawo matsala a cikin aure cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Duk namijin da ya yi iya yin sa don samarwa iyalansa abinda za su ci, bai samu ba, to ba shi da laifi har wurin Allah, domin ba shi da ikon ba wa kansa abinda Allah bai ba shi ba. Kuma a irin wannan ne aka so mata su yi haƙuri, su kuma guji tada wa mazajensu hankali kan rashi. Amma wanda yana da shi ya ƙi ba wa iyalansa haƙƙinsu na daga ciyarwa, ko ya ƙi fita ya nemo masu, to su ne mafi zalunci, kuma Allah ba zai bari lamarin ya wuce ba, matuƙar ba tuba ya yi ba, kuma ya nemi gafarar iyalan nasa.

A wannan hukunci ba inda aka tilastawa mace dole sai ta yi haquri, ta ci gaba da jure ƙuncin ba. Idan ta zauna, ta yi haƙuri don Allah, tabbas sakamakon ta zai zama abin sha’awa ga kowa, idan kuwa ta yi don gudun surutun mutane ko don kar a kirata da wani suna, to za ta ta shi a tutar babu, don ba ta da sakamako daga wurin Allah, kuma ba zata iya hana mutane kiran sunan ba a lokacin da wa’adin auren ya ƙare, wanda Allah ne kawai mai iya ƙarar da shi.

Kafin komai, zan fara daga kan dalilin da ya sa ki ke zaune da mijinki, wato don kar a kira ki da bazawara. Idan wannan ne kawai dalilin da ya sa ki ke haƙuri da mijinki, to Ina mai tabbatar mi ki kin yi asara, saboda duk wani aiki da za ki yi ba don Allah ba ba shi da lada, sakamakon da yake da shi na hannun mutane da ki ka yi domin su, kuma mai wucewa ne, don a ranar da mijin naki ya sake ki, duk haƙurin da ki ka yi ba zai hana mutane faɗa maki abinda ki ke tsoro ba. Kinga kuwa kin yi hasara.

Shawara ta farko da zan ba ki ita ce, ki tsarkake niyyarki, idan za ki yi haƙuri da gallazawar gidan aure, to kada ki yi don kowa sai don Allah. Wannan zai sa ki rabautu, ya ba ki ladar haqurin ibada, Ya yi ma ki sakayya tun a nan gidan duniya. Kuma wannan ne zai sa ki tarar da tarin lada na wannan haƙurin.

Shawara ta biyu, ki nema wa kanki mafita, domin a yadda na lura cin zarafin da mijin naki ke ma ki gaba yake yi ba baya ba. Don haka ki fara da neman zaɓin ubangiji kan ya yi ma ki mafita, idan zaman ne alkhairi ya shiryar ma ki da mijinki. Bayan nan ki kawar da zancen rashin son a kira ki da bazawara don wannan ba zai taimaki lafiyarki a lokacin da ya ma ki lahani ba, kuma ba zai ba ki lada ba, domin ba ki yi don Allah ba.

Musulunci bai tilasta wa mace zama da miji da ke yi mata irin wannan cin zarafi ba, kuma ya ba ki damar fita daga auren, don haka ni a nawa gani, ki sanya manya a cikin zancen matsalarki, idan sun fahimci halin nasa ba mai canzawa ba ne, to ba wata mafita da ta wuce rabuwa. Zancen mutane kuwa ba za ki taɓa yi masu daidai ba, ko ba su zage ki ta wannan vangare ba, za su iya samun wata kafar, don mutum ba a iya masa.

Zancen laƙani da ki ka yi kuwa, ba ni da shi, kuma ban san inda ake samun sa ba, ko da Ina da kuwa, ban taimake ki ba idan na ba ki, saboda matsalarki ba aba ce da ta ke buƙatar laƙanin da wata ƙila ma ba zai yi tasiri ba, ko ya yi ma ƙila na ɗan lokaci ne.

Zama bazawara ba aibu ba ne, matuƙar dai kin san ba laifinki a rabuwar auren. Ki bar mutane da abinda za su faɗa, ki gyara tsakanin ki da ubangijinki, don shi ne kawai mai hurumin hukunta ki ko ni’imta ki.