Gudun hijira: Mutum milyan 2.6 suka rasa matsuguni a faɗin Nijeriya – cewar Hukuma

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa ta bayyana cewa a halin yanzu kimanin mutum milyan 2.6 ne suka rasa matsugunansu a faɗin ƙasa.

Kwamishinan hukumar, Bashir Mohammed ne ya sanar da hakan a Litinin da ta gabata yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin abinci ga mutum 7,500 waɗanda ibtila’i ya shafa a fadar gwamnatin jihar Kano.

Garba ya ce ‘yan gudun hijirar da ake da su a Kano mutane ne waɗanda matsalar tsaro da ambaliyar ruwa suka shafa daga jihohin Kudancin ƙasa.

Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta kammala shirinta na sake tsugunar da waɗanda lamarin ya shafa daidai da nauyin da aka rataya wa hukumar.

Yayin da yake ƙaddamar da shirin, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce mutum 47,616 ne suka fuskanci ibtila’i mabambanta a jihar Kano.

Daga nan, Ganduje ya yaba da tallafin da gwamnati ta raba wa ‘yan gudun hijirar da ke Kano, inda shi ma ya yi alƙawarin bada gudunmawar fili kadada 20 ga hukumar don ta gina wa wadanda lamarin ya shafa matsuguni.