Gudunmawa da soyayyar Sarauniya Elizabeth II ga wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta rasu tana da shekaru 96 a duniya, inda ta shafe shekaru 70 a kan karagar mulki, inda ta tavo dukkanin al’adun Birtaniya, ciki har da wasan ƙwallon ƙafa.

Sarauniyar ta kasance jigo a wasu manyan lokuta a tarihin wasanni, musamman na ƙwallon ƙafa a Birtaniya.

Daga gabatar da gasar kofin duniya na farko a Ingila ga Sir Bobby Moore a 1966, zuwa karrama ’yan wasa da dama waɗanda suka kasance fitattun jaruman ’yan wasa ne, zuwa kasancewarta jigo a wasan ƙarshe na kofin FA.

Akwai ma jita-jitar cewa sarauniyar ya riƙe matsayi babba na ɗaya – ko wataƙila ma biyu na ƙungiyoyin Firimiya a lokacin rayuwarta. A taƙaice dai, ana kallon sarauniyar a matsayin ƙashin baya ga wasanni a Birtaniya.

Gabatar da gasar kofin duniya ta 1966:

Shekaru goma sha uku bayan naɗin sarautarta, Sarauniya Elizabeth ta yi farin cikin gabatar da Jules Rimet Trophy ga tawagar Ingila da ta yi nasara a gasar kofin duniya a 1966.

Lokacin da ta ke tunani game da bikin a cikin 2020 gabanin wasan ƙarshe na gasar kofin Turai, ta rubuta cewa, “shekaru 55 da suka gabata na yi sa’a na gabatar da gasar kofin duniya ga Bobby Moore kuma na ga abin da ake nufi da ‘yan wasa, gudanarwa da ma’aikatan tallafi don isa da nasara a wasan ƙarshe na babbar gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa.

Ba kamar sauran sarakuna ba, Elizabeth ba ta taɓa bayyana ƙungiyar ƙwallon ƙafa da ta fi so a bainar jama’a ba.

Duk da haka, hakan bai hana jita-jitar da ake yaɗawa na cewa ta kasance mai goyon bayan ƙungiyar West Ham ba. Kamar yadda jaridar The Mirror ta ruwaito a shekara ta 2009, da alama sarauniyar ya bayyana soyayyarta ta sirri ga Hammers lokacin da wani mamba a gidanta ya gaya mata cewa shi mai goyon bayan Millwall ne.

A baya, an kuma nuna cewa, Sarauniyar ta kasance mai goyon bayan Arsenal.

Girmama ‘yan wasan ƙwallon ƙafa:

Ɗaya daga cikin muhimman ayyukan al’adu na Elizabeth shine sanin irin gudunmawar da ’yan wasan ƙwallon ƙafa daban-daban suka bayar a bikin karramawar sabuwar shekara da na ranar haifuwar Sarauniya.

Stanley Matthews shi ne ɗan wasa na farko da ya samu kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa, kuma manyan jiga-jigan ƙwallon ƙafa irin su Alf Ramsey da Alex Ferguson da kuma Bobby Robson suka bi shi a shekarun baya.

Yawancin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa sun karɓi kyautar OBE, MBE da CBE, kamar Roy Hodgson, David Beckham da, kwanan nan, Gareth Bale.

Ganawa da Arsenal bayan buɗe filin wasa na Emirates:

An tsara Elizabeth ta buɗe sabon filin Arsenal, filin wasa na Emirates, a cikin 2007, amma daga baya wani abu ya hana hakan faruwa.

Gabatar da gasar cin kofin FA:

Ana yawan ganin sarauniyar a gasar kofin FA a farkon shekarun mulkinta. Ta na da muhimmin aiki, kamar a 1966, na gabatar da kofin ga kyaftin ɗin da ya yi nasara a Wembley.

Har ila yau, ta kan kasance a can don gabatar da wasu kalamai na ƙara ƙarfin gwiwa ga tawagar da suka yi rashin nasara a wasan ƙarshe.

Duk da cewa, ta fito sau da yawa a wurin wasanni a cikin shekarun mulkinta, yawancin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa sun yi la’akari da cewa haɗuwa da Sarauniya Elizabeth na ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi dacewa a cikin rayuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *