Gudunmawar harshe da al’ada ga bunƙasa tattalin arziƙi da zaman lafiya (2)

Daga FARFESA SALISU AHMAD YAKASAI

Harshe ba shi da alaƙa da mutum, wato ba wai haihuwar mutum a awuri ke sa ya ji harshen su mutanen wurin ba, sai dai idan ya tashi da amfani da shi. Saboda haka, duk wanda ya tashi da wani harshe, to lallai harshen zai koya. Jinin mutum ba ya da alaƙa da harshensa, domin sai a samu Baturen Ingila yana Larabci, ko kuwa Bafaranshe yana Hausa. Kenan furucin mutum ba ya nuna qabilarsa, domin furuci ba manunin ƙabila ne ba sai dai idan mutum ya faɗi ƙabilarsa, tun da duk inda mutum ya tashi, furucinsu zai koya ya kuma iya. Sai dai kuma furuci yana nuna matsayin mutum da iliminsa, amma ba asali da jini ba. An kuma yi amanna da cewa Bahaushe zai yi Hausa, Balarabe kuwa ya yi Larabci, Bafillace zai yi Fillanci da dai sauransu, amma ba dole ba ne.

Harshe da Al’ada a Matsayin Madubin Al’umma Al’umma ita ce tarin ƙaiƙaikun mutane da suke zaune a gari guda ko yanki ko lardi ko jiha ko kuma ƙasa. Al’umma tana iya ƙunsar ƙabilu daban-daban.

Wannan ya nuna cewa duk inda aka sami fiye da Ɗan’Adam guda a wuri guda, to lalurar hulɗa da mu’amala ta kama. Hulɗa da mu’amala kuwa basa cika ba tare da magana ba. Kenan amfani da harshe da al’ada tilas ne a hulɗa, kuma lalura ce. Tun da yake haka ne kuwa, to bukatar harshe da al’ada ga Ɗan’Adam ta kai ƙarfin bukatarsa ga abinci da ruwa, ko ma watakila har da iskar shaƙa (Rufa’i, 1986).

Ta hanyar harshe, ana iya samun hasken tarihin al’umma. Wato ta harshen al’umma ne akan iya gane ci gabanta musamman dangane da tsarin mulki ko shugabanci da sharia da ilimi da tattalin arziƙi da addini da kuma al’ada. Sauran maganar kuma ita ce, idan aka yi dace cewa al’ummar tana da hanyar rubutu, to ta rubuce-rubucensu za a ga gacin da suka kai domin a ci gaba. Idan kuma babu hanyar rubutu, to ta hikimarsu ne kawai za a iya ganewa cikin mu’amala da su. Ta adabin al’umma ma ana iya gane irin ƙwazonsu cikin tarihi.

Ta nan ne wayonsu zai bayyana da kuma ƙoƙarinsu na kyautata rayuwarsu da irin gudummawar da suka bayar wajen ci gaban al’umma. Domin qara tantance dangantakar harshe da al’ada, da kuma yadda sakamako ko kuma tasirin wannan dangantaka ke zama matsayin madubin al’umma, bari mu ɗan yi nazarin jigogin rayuwar al’umma.

Amfani ko kuma fa’idar yin nazarin shi ne fito da bayanan dangantakar a tsakaninsu. Da yake sadarwa tsakanin al’umma lalura ce wajiba, bukatun rayuwa za su matsa wa ‘yan wata ƙabila su yi hulɗa ko mu’amala da ‘yan wata ƙabula daban. Hakan ya zama dole domin ita hulɗa ko mu’amala ba ta yiwuwa sai fa ta amfani da harshe cikin dangantaka da al’ada.

A taƙaice dai idan ana magana a kan matsayin harshe da al’ada na madubin al’umma, to wajibi ne batutuwa irin su koyar da harshe da ilimantarwa da tattalin arziƙi da tsarin zamantakewa da kuma nishaɗantarwa su bijiro.

Nazarin Jigogin Rayuwa. Da yake al’umma ta ƙunshi ƙaiƙaiku, to ashe al’umma aba ce rayayyiya wacce take da farko da halin rayuwa da kuma ƙarshe, ko kuma a cikin hikima a iya cewa al’umma tana da jiya, tana da yau kuma tana da gobe.

A ra’ayin Rufa’i (1986), idan aka juya ta wata hanya, to muna iya cewa al’umma tana da tarihi, kuma a cikin wannan halin wanzuwar tana yaƙin rayuwa. Bugu da ƙari kuma, tana faman tabbatar da kyawawan abin da zai je ya zo.

Wannan ya nuna cewa al’umma kamar tilon Ɗan’Adam tana da alfahari da kuma buri. Alfaharin nan shi ne tarihi, buri kuwa shi ne kokawar rayuwa domin yau da kullum. Saboda haka, a fafutuka ta wanzuwa, akwai bukatar abubuwan nan da suka zama dole ga kowace al’umma domin rayuwa. Waɗannan abubuwa su ne: mulki da sharia da tattalin arziƙi da ilimi da addini da kuma al’ada. Tsarin mulki a cikin kowace al’umma wajibi ne.

Mulki shi ne kaƙai zai tabbatar da zaman lafiya yadda kowa zai sami damar yin harkokinsa na yau da kullum domin neman abinci da arziƙin duniya. Wato idan babu mulki a al’umma, to ruɗani da yamutsi da hargitsi da kuma cutar juna ne za su tabbata. Idan haka ya auku, sai al’umma ta kai ga halaka domin babu wanda zai sami sukunin neman abinci ballantana arziƙin ƙasa.

Domin a sami cikakkiyar lumana da tabbatar da zaman lafiya, ya wajaba a sami fahimtar juna tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka. Mafi yawan kyawun hanyar fahimtar ita ce harshe wanda muka ce shi ne jigon sadarwa. Ga misali, kafin zuwan Tuarawa ƙasar Hausa, mutane ne daga cikinmu suke mulkin ƙasarmu. Wato harshenmu ɗaya da su, kuma duk hanyoyin rayuwa ɗaya ne tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka. Don haka, sadarwa take da sauqi, wanda hakan ya tabbatar da bin umurni da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali.

Daga nan Nasara ya ƙwace mulki, amma kuma harshenmu da na nasara ba ɗaya ba ne. Don haka sadarwa tsakaninsa a matsayinsa na mai mulki, da, mu a matsayin waɗanda ake mulka sai ta wuyata. Gaskiyar maganar ita ce, a yayin da aka rasa sadarwa tsakanin mai mulki da kuma wanda ake mulka, to babu yadda shi wanda ake mulka ɗin zai sami damar sa baki a yadda ake mulkin nasa.

Sauran maganar ita ce, zuwan Baturen ne dai ya kawo mana tsarin mulki na siyasa wanda hasken saninsa yana cikin harshen da ba namu ba. Haka kuma Bature ya bar mana gadon tsarin mulki wanda a kan rubuta shi da harshen da ba na ‘yan ƙasa ba ne. Kasa fahimtar waɗannan abubuwa ya kawo matsala.

Bayan tsarin mulki, kowace al’umma ba za ta gaza bukatar tsarin Sharia ba, da yadda za a tabbatar da adalci a mulki. To a nan ma harshe yana da rawar da za a gani. Wajibi ne ga jama’a su fahimci irin shariar da ake yi a ƙasarsu domin su tabbatar wa kansu adalci idan rigima ta same su.

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *