Gudunmawar kamfanonin fasahar sadarwar ƙasar Sin ga ƙara dunƙulewar duniya

Daga SAMINU HASSAN

A wannan lokaci da muke cikin yanayi na dunƙulewar al’ummun duniya wuri guda, hidimomin sadarwa na da matuƙar muhimmanci, kasancewar suna buɗe ƙarin ƙofofin raya tattalin arziki, da kyautata zamantakewar al’ummu daban daban.

Kaza lika damar sadarwa tsakanin al’ummun duniya ta riga ta zama ɗaya daga cikin hidimomi masu daraja na more rayuwar bil adama.

Hakan ne ma ya sa ƙarƙashin kyawawan manufofin ƙasar Sin, gwamnati ke ƙarfafa gwiwar sassa daban daban, musamman kamfanonin ƙasar da su tallafa, wajen bunƙasa samar da ababen more rayuwa ga al’ummun duniya a duk inda suke.

A baya bayan nan, kamfanin ayyukan fasahar sadarwa na ƙasar Sin wato Huawei, ya alkawarta haɗe sassan al’ummun duniya miliyan 120, dake rayuwa a wurare masu wuyar kai wa, a ƙasashen duniya da yankuna sama da 80 da layukan sadarwar wayar tafi-da-gidanka, nan zuwa ƙarshen shekarar 2025.

Fatan kamfanin shi ne ƙara faɗaɗa gajiyar sadarwar wayar hannu ga al’ummun duniya, ta yadda za su ci riba daga fasahohin bunƙasa tattalin arziki, da kasuwanci, da inganta sha’anin zamantakewa, da dasa tunani mai kyau a fuskar samar da ci gaba mai ɗorewa.

Dama dai ya zuwa ƙarshen shekarar 2021, kamfanin na Huawei, ƙarƙashin shirinsa na “RuralStar telecom solutions”, wato shirin samar da turakun sadarwar salula a kauyuka, ya rika ya haɗa sama da mutum miliyan 60 dake rayuwa a wurare masu wuyar shiga, a ƙasashe da yankunan duniya sama da 70 da layukan wayar hannu.

Ba shakka irin wannan tunani, na faɗaɗa damar al’ummun yankunan karkara, da mutanen dake zaune a wurare masu nisa, na samun hidimomin wayar sadarwa da kamfanin Huawei ke aiwatarwa abun a yaba ne.

Kuma wata muhimmiyar hanya ce da kamfanonin Sin ke bi wajen ingiza bunƙasuwar tattalin arzikin al’ummun duniya, musamman al’ummun ƙasashe masu tasowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *