Gudunmawar sarakunan Ƙasar Nijar wajen bunƙasa al’adu da zaman lafiya

Daga WAKILINMU

Wannan rubutu ya samo asali ne daga wani kira da wani ɗan uwa marubuci Usman Mani Kusumawa Kargeri, ya yi min game da cewa ya kamata na yi ɗan rubutu game da sarakunan ƙasarsu ta Nijar game da hibbarsu da kuma adalcinsu ga duk wanda ya kusance su, sakamakon yadda wasu mutane suke ganin cewa Masarautar Agadez ba ta kyauta ba don ta hana ’yan fim ɗin Hausa (Kannywood) zuwa ƙasarta da sunan shirin fim, saboda wani fim da kamfanin ‘2Effect Empire’ suka shirya mai suna ƊAN SARKIN AGADEZ, fim ɗin da ya gaza cimma manufar saƙon da ake son nunawa jama’a, hasalima fim ɗin tozarci ne ga masarautar da al’adunta.

Babu shakka masarautun ƙasar Nijar kaffatanninsu masarautu ne masu cike da haiba da kuma ɗimbin tarihi kuma masu adalci ga al’ummar da suke shugabanta.

Duk mutumin da ya kasance mai bibiyar tarihi zai yarda kuma har ma ya aminta cewa sarakunan ƙasar Nijar ba su da kyashi ko baiken jin cewa sun taimake ka wajen samar da tarihi da kuma labarin da abin da ya shafe su, kamar yadda na zama ganau ba jiyau ba kamar yadda hausawa ke azancin magana da cewa wai ‘Gani Ya Kori Ji’.

Bari na fara da Masarautar Sultan ta Damagaran a shekarar 2014 na ziyarci fadarsa a wani rangaɗin bincike da nake yi wanda zai kai ni har gaba da Agadez, Sultan Abubakar Sanda wanda yake mulkin ƙasar Zinder ya yi matuƙar farin ciki da zuwa na ya kuma bani masauki tare da bani cikakken lokacin da muka zanta da shi na wani dogon lokaci, har ya gayyace ni zuwa tarbar Ministan cikin gidan ƙasar wanda zai kawo ziyarar aiki a jihar, amma rashin lokacin da ba ni da shi ban samu damar amsa gayyatar ba, don a daidai lokacin yakamata a ce na isa Agadez akan lokaci, bai damu ba ya yi min wannan uzuri sannan ya bani saƙon gaisuwa zuwa ga takwaransa na Agadez wato Sultan Ouamar Ibrahim Oumar na Agadez mun yi bankwana da fatan idan na dawo na sake biyawa fada na sanar da shi, hakan kuwa aka yi bayan na dawo na biya masa abin mamaki sha tara arziki aka min a wannan fada cikin barkwanci da raha sosai mu ka yi bankwana da shi da duk mutanen fadar.

Har ila yau daga cikin karamcin wannan sarki shi ne ya ɗauki nauyi taron ƙaddamar da ƙungiyar haɗaka ta ƙasashen Afrika mai suna ‘GIDAUNIYAR ZUMUNCI’ tare da bikin al’adun Hausawa na duniya a jihar Zinder a wannan shekara ta 2018.
Haka ma jihar Agadez bayan na isa masarautar na sanar da Sultan zuwana sai na wuce zuwa masaukina don hutawa saboda gajiyar hanya, bayan kwana ɗaya da zuwa na, ina barci da rana Sultan ya aiko yana son za mu gana ta hanyar Yariman Agadez Malam Ousseini ɗan Abbo, Sultan na Agadez mutum ne mai cike da kwarjini da haiba ga izza wadda za ta nuna ma ka shi cikakken sarki ne mai daraja ta farko, duk da cewa mu huɗu ne a fadar ta shi amma baya magana da ni kai tsaye hasalima bana jin abin da yake faɗa sai idan ya yi magana a gaya min abin da ya ce, a haka muka tattauna muhimman batutuwa, wani abin burgewa da wannan sarki shi ne son jama’ar ƙasarsa da kyautata musu, mun yi tafiya da shi zuwa dazuka (idan aka je daji a ƙasar Nijar ana nufin wasu garuruwa da suke cikin duwatsu da sahara) don halartar taron addu’a na ƙarshen shekara da ake a ƙasar don neman zaman lafiya da wanzuwar arziki a ƙasar, motarmu tana gaba ta sultan tana bayanmu sai muka wuce wasu mata da ƙananan yara a hanya ga dukkan alamu wani garin da ke gaba da su za su je, a cikin motarmu sai sakataren Malaman Jihar Agadez Malam Namadina Alhaji Ousseini ya ce, “zai wahala Sultan bai tsaya yasa a ɗauko mutanen nan ba”, haka kuwa aka yi ba mu yi nisa ba sai muka ga ana alamta mana cewa mu dakata, bayan mun tsaya muka dawo baya sai muka ga Sultan ya sauko da kansa ya sanya an ba waɗannan mutane mota guda wadda ta ɗauke su tare da kayansu ta kai su garin da za su je.

Wannan abin ya matuƙar burgeni na kuma ji na ƙara ƙaunar wannan sarki. A tsawon kwana uku da muka yi a dajin nan wallahi kusan ko yaushe duk abin da aka kai wa Sultan sai ya sanya an kawo mana da yake masaukanmu suna daf da juna. Bayan an kammala waɗannan addu’o’i ba fadarsa ya dawo ba sai da ya wuce zuwa wasu garuruwa don ya gansu ya kuma tattauna da su, bincikena ya gano cewa wannan sarki kusan koyaushe yana cikin waɗannan ayyuka na ziyarar mutanensa da kuma gabatar da ayyukan da suka shafi ci gaban ƙasarsa duk da cewa akwai sarkin da aka sanya don lura da waɗannan garuruwa da ake kira A’ir mai suna Muhammad Suleyman Anastafident, bayan mun dawo sarkin ya sake tambayata akwai wani abu da nake buƙata wanda ban samu ba? Na amsa da babu duk wani aiki da ya kai ni na kammala shi har da ma ribar ƙafa.

A ɓangaren mutanen Agadez da Nijar kuwa babu wani abu da zan bayyana su da shi sai dai na ce su mutane ne masu son jama’a da kuma girmama baƙi da ƙaunar junansa, wani abu da ya sa nake ƙara yaba musu shi ne yadda suka riƙe al’adunsu da kuma girmama tarihinsu.

A shekarar 2016 ma na ziyarci fadar sarkin Maradi tare da wani babban ɗan kasuwa da ke Nijeriya don buɗe reshen harkar kasuwancinsa garin Maradin babban abin da ya burge ni shi ne yadda mutanen fadar suka karɓe mu da karamci tare nuna jin daɗinsu game da wannan abin alheri da zai zo ƙasarsu, haka ma mahukunta jihar su ma sun nuna jin daɗinsu don har wakilin gunduma ya ba mu gayyata ta musamman zuwa gidansa amma da yake muna sauri za mu wuce zuwa Niamey ne, ba mu samu zuwa ba, a wannan ɓangare ma na yaba musu kwarai.

A saboda a haka a matsayina na Marubuci kuma Ɗan Jarida na ke roƙon duk wani marubuci ko ɗan Jarida kai har ma da masu shirya fim su kasance masu bibiyar tarihi da bincike tare da bibiyar masana kafin yin duk wani aiki wanda zai shiga hannun jama’a saboda gudun irin abin da ya faru a baya game da Fim ɗin Ɗan Sarkin Agadez, da ma wasu daga cikin rubuce-rubucenmu, Allah Ya jiqan marigayi Gambu mijin Kulum. Mun taɓa haɗuwa da shi a jami’ar jihar Kaduna muna zantawa yake nuna min rashin jin daɗinsa da abin da wani marubuci yayi masa na rashin adalci, ya ce marubucin ya rubuta ƙarya game da shi da sunan tarihinsa ba tare da kyakkyawan bincike ba.

Bana mantawa lokacin da na ziyarci wata faɗa a ƙasar Nijar ɗin dai ta sarki Ahmad Aghali Ibbah sarkin Tanhiya sun sanar da ni tarihinsu tare da cewa duk abin da suka gaya min haka zan rubuta kar na rage kar na ƙara, kun ga wannan ai shi ne adalci, wani abu da ya sake burgeni da mutanen ƙasar shi ne lokacin da na je shan ruwa wajensu an samu matsala, amma da na bayyana musu cewa ni baƙon sarki ne sai suka kyale ni na tafi abina. (Cikakken rahoton yana cikin labarin ziyararmu birnin Tanhiya) A nan ma ya nuna cewa wannan sarki zaune yake da al’ummarsa lafiya suna ƙaunarsa yana ƙaunarsu.

Da fatan wannan tsokaci zai sanya mu amfana wajen yin abin da zai zama karɓaɓɓe a kan komai da za mu yi.

Mun gode ƙwarai.