Guguwa mai ƙarfi ta halaka mutane biyu da lalata gidaje 20 a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ringim ta jihar Jigawa, Shehu Sule-udi, ya ce mutane biyu ne suka mutu a wata guguwa da ta afku a ranar Litinin a yankin.

Sule-udi, wanda ya yi magana kan lamarin a wata hira da manema labarai a ofishinsa a ranar Laraba, ya ce guguwar ta kuma lalata gidaje 20.

Ya ce ta kashe mutanen ne a unguwar Larabawa da Hambarawa.

Ya ce lamarin da ya faru da tsakar dare ya sanya ‘yan garin da dama suka rasa matsuguni.

Shugaban Ƙaramar Hukumar ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da damuwa sannan ya yi alƙawarin taimakawa waɗanda abin ya shafa.

Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa, waɗanda suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya sun yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su tallafa musu.

Aminu Hadi, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa da suka rasa gidajensu, ya bayyana lamarin a matsayin mai ƙarfi da ban tsoro.

Hadi ya nemi tallafi daga masu hannu da shuni, ƙungiyoyi da gwamnati domin a kawo musu ɗauki.

Ya kuma yaba wa Ƙaramar Hukumar bisa kawo musu ɗauki tare da bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *