Gumi ya shiga tsakani don neman kuɓutar da ɗaliban Kagara da aka sace

Daga AISHA ASAS

Alamu da dama kuma masu gamsarwa sun nuna fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Ahmed Gumi, ya shiga tsakani domin kuɓutar da ɗaliban nan su 27 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kagara, Jihar Neja, cikin wannan makon.

Bayanai daga jihar Neja sun tabbatar da Sheikh Gumi ya ziyarci Neja ya samu ganawa da ‘yan bindigar da suka kwashe ɗaliban a dajin Bangi a ranar Alhamis.

Idan da dai za a iya tunawa, a daren Larabar da ta gabata ‘yan bindigar suka kai hari a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a yankin ƙaramar hukumar Rafi, inda suka kwashe ɗalibai da sauransu.

Binciken Manhaja ya gano cewa malamin ya yi tattauna mai zurfi da ‘yan bindigar kafin cim ma wata matsaya.

Da ma dai sai da malamin ya ziyarci gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, bayan aukuwar lamarin inda suka yi tattaunawar sirri. Bayan haka ne malamin ya tafi ya gana da ‘yan bindigar kamar dai yadda majiyar Manhaja ta bayyana.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani bayani a hukumance dangane da sakamakon ganawar da Sheikh Gumi ya yi da ‘yan bindigar.