Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta bayyana aniyarta na rarrabe makarantun ɗalibai maza da na mata, la’akari da yadda gurɓacewar tarbiyya ta kasance ruwan dare a tsakanin makarantun ta na sakandare a ɗaukacin cikin jihar.
Kwamishina mai lura da lamuran ma’aikatar, Dokta Aliyu Usman Tilde da yake bayyana wannan aniya ta gwamnati a garin Bauchi jiya Alhamis, ya nuna matuƙar damuwar gwamnatin jiha bisa yadda tarbiyyar ɗalibai a makarantunta ya kasance abin kaico.
Dokta Aliyu Tilde ya bayyana cewar, “wannan shiri na makarantun mata zalla da na maza zalla tsohon shiri ne da a yanzu ma’aikatarsa take ƙoƙarin faɗaɗa shi, ya shafi wasu nau’i na makarantu, domin lokacin da aka fara shirin babu makarantun jeka-ka-dawo.
“Shiri ne wanda aka ɓullo da shi tun shekarar 1978, a lokacin babu makarantun jeka-ka-dawo sai na kwana, shine ya sanya har zuwa wannan rana Jihar Bauchi take da makarantun kwana na mata da na maza daban-daban.”
Tilde ya yi waiwaye da cewar, an fara samar da makarantun jeka-ka-dawo ne a lokacin gwamnatin siyasa a jumhuriya ta biyu ta tarayyar Nijeriya, kimanin shekaru 40 kenan da suka shuɗe, kuma ganin a tsawon wannan lokaci, ɗaliban makarantun jeka-ka-dawo suna kwana a gidajen iyayen sune ake ganin tarbiyyar su ba lalatacciya ba ce.
“Amma da tafiya ta yi nisa ya zuwa mulkin Ibrahim Babangida, sai makarantun jeka-ka-dawo suka cigaba da yawaita, la’akari da hauhawar bukatu na yara masu shiga makarantu. Kuma cikin waɗannan lokuta abubuwa da suke faruwa a makarantun mu na sakandare, ban isa na faɗe su ba, abubuwan babu daɗin ji.
“A yanzu kafofin sadarwa na zamani sun buwayi al’umma. A baya idan za ka yi magana da mutum ta hanyar waya, za ka ji muryarsa ne kaɗai, a zanzu za ka gan shi murara kana magana da shi. Kuma za ka iya yin magana da kowane jinsin mutum dake nan cikin faɗin duniya, walau ka waye da shi ko akasin haka.”
Tilde ya ƙara bayyana cewar: “A yanzu mutum zai iya bidiyo daga kowane sashi na duniya, gashi kuma munanan ɗabi’u na duniya sun karaɗe al’ummai, sun shiga jikkunan waɗannan ɗalibai da suke cikin shekarun haɗari, shekarun balaga, jikkunan su suna canjawa a gaggauce, sa’annan ba su ma fahimci yadda za su fuskanci waɗannan canje-canje ba.”
Kwamishina Tilde, don haka ya ce ire-iren ma’aikatun su ba su kamata a riqa kiran su ma’aikatun ilimi ba, kamata ya yi ake kiransu da sunayen Ma’aikatun Koyar da Ilimi da Nusar da Tarbiyya, da zummar cewa ɗaya daga cikin haƙƙoƙin al’umma dake kan waɗannan ma’aikatu shine na taya iyaye wajen tarbiyyantar da ‘ya’yan su a lokuta da suke cikin makarantu.
Tilde sai ya kalmashen bakin jakar da cewa, “a lokuta da waɗannan ɗalibai suke cikin makarantu, wajibi ne mu tabbatar cewa, basu gamu da wasu munanan abubuwa ba, balle su yi koyi da su, harma su riƙa komawa gidajensu da su. Wannan nauyi shine muke yin ƙoƙari mu sauke, kuma wajibi ne mu sauke shi a halin yanzu, ganin yadda lamura suka lalace.”