Gurɓatattun gwamnoni na shirin tserewa kafin rantsar da sabuwar gwamnati – EFCC

Hukumar EFCC ta bayyana cewa, wasu da ake zargin gurɓatattun gwamnoni da ‘yan siyasa na shirin ficewa daga Nijeriya kafin ranar 29 ga Mayu inda za a rantsar da sabuwar gwamnati.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, 19 ga Mayu, 2023.

EFCC ta ce tuni ta fara haɗa kai da takwarorinta na ƙetare domin tabbatar da haƙar gurɓatattun ‘yan siyasar ba ta cimma ruwa ba.

Hukumar ta sha alwashin tabbatar da dukkan gurɓatattun ‘yan siyasar sun girbi abin da suka shuka sa’ilin da suke riƙe da madafun iko.

“Hukumar na sanar da al’umma game da shirin da wasu da ake zargin gurɓatattun ‘yan siyasa ne ke yi na neman tserewa daga ƙasar gabanin 29 ga Mayu.

“Hukumar na aiki tare da takwarorinta na ƙetare don daƙile shirin nasu da kuma tabbatar da dukkan waɗanda lamarin ya shafa sun fuskanci hukunci,” in ji sanarwar.