Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mahukunata a Nijeriya sun yi nasarar gurfanar da mutane 100 da ake zargi da ɗaukar nauyin ta’addanci a cikin shekaru biyu da suka gabata a cewar sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata.
Akume ya bayyana hakan ne a wurin wani taron gangamin yaƙi da safarar haramtattun kuɗi da masu ɗaukar nauyin ta’addanci da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke ɓilla a Abuja wadda Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta ƙasa, (NFIU) ta shirya.
“Mun samu cigaba mai yawa wajen magance barazanar ayyukan ta’addanci da munanan laifuka ta hanyar rundunar jami’an tsaronmu da ke bakin daga,” ya bayyana.
“Sannan ta hanyar dabaru na hukumar tattara bayanan sirri, mun samu cigaba wajen bankaɗo ɗaiɗaikun mutane da ke ɗaukar nauyin munanan ayyuka da taimakon ofishin mai ba wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan tsaro da ofishin antoni-janar na ƙasa. Sannan mun gurfanar da mutane 100 da suka ɗauki nauyin ta’addanci a shekaru biyu da suka gabata,” inji Akume.
Sakataren gwamnatin ya ce, gurfanar da waɗanda suke ɗaukar nau’yin ta’addancin wani ɓangare ne na irin nasarorin da gwamnatin shugaban ƙasa ke samu.
Sannan ya ce ta hanyar dakatar da kuɗin da kayan aikin da ƙungiyar Boko Haram da ISWAP ke samu, gwamnatin na hana su ne samun damar cigaba da addabar al’umma da kuma bai yankunan karkara damar farfaɗowa domin samun cigaba.
Akume ya ce wannan salo na bibiyar kuɗi muhimmiyar dabara ce ta yaƙi da ta’addanci da laifuka a duniya. “wannan ce dabarar da muke amfani da ita wajen yaƙi da manyan laifuka a Nijeriya. Kenan bayan ayyukan ta’addanci, muna ƙoƙarin kawar da sauran manyan laifuka da ake yi.”
A yayin da take magana a wurin taron, babbar shugabar hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa, Hafsat Bakari, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su haɗa kai da hukumar wajen rage da kare tsarin tafi da kuɗi a Nijeriya.
“Yaƙin da ake da laifuka da suka shafi kuɗi, abu ne da hukuma ɗaya ba za ta iya cimma nasara ba. Abu ne da ke buƙatar haɗin kai da jajircewa daga shugabanni da masu sa-ido da cibiyoyin tafi da lamuran kuɗi da jami’an tsaro da sauran abokan hulɗa na ƙasashen waje.”
“Haɗin kai shi ne ginshiƙin tsarin kai wa ga nasara wajen rage barazanar da ake fama da ita a ɓangaren kuɗi,” ta bayyana.
Ta ce, zuwan mahukunta daban-daban daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da masu zaman kasu, ya nuna irin ƙarfin da haɗin kai ke da shi wajen samun nasara.
Ta kuma nuna damuwarta game da rahoton haɗin guiwa na na ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta yaƙi da Safarar Haramtattun Kuɗaɗe ta Yammacin (GIABA) wacce ta bayyana wasu wurare da Nijeriya ke da buƙatar ingantawa. Ta ce waɗannan wurare ne suka sanya Nijeriya cikin waɗanda har yanzu ke fuskantar barazana ta safarar kuɗi.”
“Hukumar NFIU tare da haɗin guiwar abokan hulɗarmu, muna ta aiki tuƙuru domin ganin mun magance ƙalubalen da ake fa da su,” a cewarta.