Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan Majalisar Wakilai, Hon. Mohammed Bello-El-Rufai (APC-Kaduna), ya yaba wa Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta 8, da kuma Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa gagarumar rawar da suka taka a fafutukar tabbatar da dimukraɗiyya a Nijeriya.
Hon. El-Rufai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa, wanda ɗan tsohon Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne, inda ya kuma yaba wa Marigayi Gani Fawehinmi, Femi Falana da sauran masu kishin ƙasa, ya bayyana hakan ne a wajen wani taron da ƙungiyar ’yan majalisar dokoki ta ƙasa (NASSLAF) ta shirya a Abuja a taro mai taken ‘Gudunmawar Mataimakan Majalisa a Cigaban ƙasa’.
Duk da cewa, a na ganin ba su jituwa da mahaifinsa, Malam Nasir El-Rufai, wanda Gwamna Uba Sani ya gada, ɗan majalisar, wanda ya kira tsohon ɗan Majalisar Dattawan a matsayin uba, ya ce, “yana ɗaya daga cikin tsofaffin manyan masu faɗa a ji tare da mai ba ni shawara, Sanata Uba Sani. Na yi farin ciki da aka gayyaci Shehu Sani a nan.
“Ba tare da la’akari da siyasar da ke tsakaninsa da mahaifina ba misali, hatta maƙiyan Sanata Shehu Sani ba za su iya watsi da gaskiyar cewa shi mazhabar marigayi Gani Fawehinmi ba, Falana sun ci gaba da bayar da shawarwari da tabbatar da walwala da haƙƙoƙin ma’aikata a faɗin duniya.”
Dangane da buƙatar kiyaye majalisar, El-Rufai ya ce, ya kamata a ɗauki ayyukan masu taimaka wa majalisa da muhimmanci. Ya yaba wa Shehu Sani da Gwamna Sani bisa yadda suke kula da mataimakansu na majalisa a lokacin da suke Sanatoci.
Mista El-Rufai ya ƙara da cewa, Sani biyu na da mataimakansu na majalisa a ofisoshin mazaɓarsu, domin bai wa jama’a ribar dimukraɗiyya, yana mai jaddada cewa “Ina son ci gaba da hakan.”
A nasa ɓangaren, Shehu Sani, wanda ya kasance babban mai jawabi a wajen taron, ya yaba wa Mista El-Rufai kan yadda ya ke gudanar da wakilci nagari a mazaɓar Kaduna ta Arewa.
Dangane da rawar da majalisar dokokin ƙasar ke takawa wajen gina ƙasa, Mista Sani ya yi kira ga buƙatar ‘yancin kan majalisar, inda ya ƙara da cewa mataimakan majalisa na taka muhimmiyar rawa wajen samun wakilci mai inganci a majalisar.
Ya yi kira ga masu taimaka wa ‘yan majalisa da su riƙa gaya wa shugabanninsu haƙiƙanin abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan.
Mista Sani ya buƙaci majalisar da ta sauke nauyin da ke kanta domin ci gaban Nijeriya da ‘yan Nijeriya.
Ya ce majalisar da ke ƙarƙashin kasa ba za ta iya yin aiki da muradun ƙasa ba, yana mai cewa hakan na iya shafar shugabanci nagari da kuma kawo cikas ga dimokuraɗiyya.
“A zamaninmu, ba zai yuwu ba shugabannin ma’aikatu su yi watsi da sammacin da muka yi. Sun fahimci nauyin ayyukan sa ido namu,” inji shi.
ɗan majalisar ya kuma shawarci ‘yan majalisar da su guji fifita abin da ya rataya a wuyansu fiye da aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu.