Gwajin ƙwayar halitta kafin aure da muhimmancinsa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Bai zama sabon labari ba, ko wata sabuwar bidi’a, yin gwaje-gwaje don tabbatar da lafiyar waɗanda ke shirin yin aure. Birni da ƙauye yanzu wannan tsari ya zama gama-gari, ko da yake ba zan ce ko ina ne tabbas ake hakan ba. Amma lallai jama’a da dama, malamai da ƙungiyoyin addini sun karɓi wannan tsari saboda muhimmancinsa, ga tsaron lafiyar ma’aurata da zuriyar da za a samu.

Muhimmai daga cikin gwaje-gwajen da ake yi su ne na sanin nau’in ƙwayar halitta wato gwajin Genotype, inda ake ƙoƙarin gane ko ƙwayoyin halittar jikin ma’auratan ya dace da samun ‘ya’ya masu ƙoshin lafiya. Sai kuma gwajin cutar HIV, wato cuta mai karya garkuwar jiki, wacce daga cikin hanyoyin da ake iya ɗauka har da ta hanyar jima’i tsakanin ma’aurata da sauran su.

Jami’an lafiya na ƙarfafa yin waɗannan gwaje-gwaje ne, domin cika ƙa’idar tabbatar da ingancin lafiyar ma’aurata kafin cika sharuɗɗan yin aure, da kuma samar wa yaran da za a haifa ta dalilin wannan aure idan Allah ya yarda, za su rayu cikin ingantacciyar lafiya da kuzari.

Da dama jama’a sun fi gane wa muhimmancin gwajin cutar HIV, saboda yadda masana kiwon lafiya suke ta ƙoƙarin wayar da kai, a asibitoci, gidajen rediyo da sauran kafofin watsa labarai, domin ganar da jama’a illolin wannan cuta da haɗarinta ga lafiyar jikin ɗan Adam, ta yadda aka samu wayewa da fahimta, birni da ƙauye. Sai dai ba kasafai jama’a suka fahimci muhimmancin gwajin nau’in ƙwayar halittar jini ba, wanda ke gadar wa ‘ya’yan da za a haifa cutar Sankarar Jini da aka fi sani da Sikila, idan ba a dace da jituwar ƙwayoyin jinin ba.

Binciken masana kiwon lafiya na nuni da cewa, akwai nau’ikan ƙwayoyin halittar jini kimanin guda biyar zuwa shida da bincike ya tabbatar da su, da suka haɗa da AA, AS, SS, CC, AC, da SC. Kowanne ɗan Adam za a iya samun sa da ɗaya daga cikin waɗannan nau’ikan ƙwayoyin halittar, waɗanda daga ciki akwai wasu da haɗuwar su take sa a haifi ɗa mai lafiya, wasu kuma haɗuwar su ta haifar da ɗa mai Sankarar Jini, saboda rashin jituwar ƙwayoyin halittar. Kamar misalin ruwa ne maiƙo, ko sinadarin makamashi irin su kanazir ko fetur. Dukkan su dai yanayin ruwa ne da su, amma halittar su daban-daban ne!

Likitoci suna cewa, idan ma’aurata masu nau’ikan halittar jini mai laƙabin AA da AA, ko AA da AS, ko kuma AA da AC suka yi aure to, yaran su sun kuɓuta daga cutar Sankarar Jini. Amma idan ƙwayoyin halittar su AS da AS ne, ko AS da SS, ko SS da AC, ko kuma SS da CC ne, ba zai yiwu su yi aure ba sam, don kuwa ƙwayoyin halittar su ba za su jitu da juna ba, za su iya haifar yara masu Sikila, wato Sankarar Jini, ko da kuwa ba dukkan su.

Yana da kyau jama’a su gane cewa, cutar Sankarar Jini cuta ce mai matuƙar haɗari ga lafiyar ɗan Adam, wacce ke hana yara kuzari ko girma kamar sauran yara, kuma suna rayuwa cikin yawan laulayi da ƙwambarewar gaɓoɓin jiki. Kuma akasarinsu ma ba sa tsawon rai.

Kawo yanzu dai ba a gano takamaimen maganin wannan mugunyar cuta ba. Sai dai ƙoƙari da masana sirrin harhaɗa magunguna ke yi na gano makarin wannan cuta. Shi ya sa likitoci ke ba da shawarar a daina gaggawar haɗa auren masoya mace da namiji da ke sha’awar aure, har sai an tantance nau’in ƙwayar halittar jinin su ta hanyar yin gwaji.

Saboda ƙalubalen da ake fuskanta wajen dakatar da auren da ake daf da ɗaura shi bayan an gano rashin jituwar jinin ya kamata a ce tun lokacin da iyaye suka tabbatar da wanda za su bai wa ’yarsu, shi ma kuma namijin iyayen sa suka tambayar masa matar da yake so har suka haɗu da iyayen ta aka tattauna tun a matakin farko to, tun kafin a kai ga matakin BADA SADAKI ko ƊAURA AURE a je a yi wannan gwajin, saboda babu wasu iyayen da za su ji daɗi a ce sai an tara mutane an haɗu don ɗaurin aure a ce a fasa, saboda sakamakon da gwajin ya bayar.

Shawara dai ga iyaye a nan ita ce tun kafin tafiya ta yi nisa yaransu su shaƙu da juna, har rabuwar su ta iya zama da matsala to, a yi waɗannan gwaje-gwajen, don sanin makamar alaƙarsu. Kada a bari sai abin ya kai wani matsayi da raba su zai zama da wahala, ko kuma ta kai matakin da za su ce tun da ba za su samu damar yin aure ba to, za su je su aikata abin da zai jefa su cikin fushin ubangiji. Ko kuma su masoyan su samu kansu cikin wata matsala da za su jefa rayuwar su cikin tsaka mai wuya!

Allah ya sa wannan faɗakarwa ta amfanar da mu, mu kiyaye kawunan mu da iyalan mu daga faɗawa cikin wata rayuwa mawuyaciya.