Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano a hukumar amintattun na asusun fansho na jihar Kano, Hon. ɗalhatu Bichi ɗan Yellow, ya bayyana cewa duk wanda yake Kwankwasiyya yake a jam’iyyar NNPP yana kan tsari ne na biyayya.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ƙaddamar da biyan kuɗin garatuti karo na uku da Gwamna jihar Kano ya yi a gidan gwamnati, ya ce shi ya sa su a matsayin su na matasa a tsarin Kkwankwasiyya kullum suke cewa Gwamnan jihar Kano da jagoransu na Kkwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso su gode wa Allah bisa yadda kullum suke dasa ayyukan alkhairi yara ƙanana da su matasa da suka ɗan tasa har suna riƙe wasu muƙamai da wasu damarmaki suke koyi da irin kyawawan halaye da suke gani daga gare su a aikace.
Hon. Yellow ya ce a harkar siyasa da suke akwai maƙiya da basa son ganin irin ci gaba da tsarin kwankwasiyya ke kawowa al’umma, saboda haka za su iya faɗar duk wani abu da za su ɓata sunan tafiyar Kwankwasiyya sai dai ba za suyi nasara ba, domin ayyukan ci gaba da Gwamnatin Abba ta kwankwasiyya take a bayyane suke kuma duk wani mai aikata alkhairi a Kano ɗan Kwankwasiyya ne.
Ya ce biyan kuɗin ‘yan fansho da Gwamnan jihar Kano yake na ɗaya daga alƙawarurruka da ya yi lokacin da ya zaga ƙananan hukumomi 44 yaƙin neman zaɓe ciki har da na biyan ‘yan fansho duba da irin zalunci da ake musu a gwamnatin baya na cire musu kuɗaɗen su na wata da hana su garatuti, idan ma za a ba su sai an bi ta kan wata mata ko ‘ya’ya sun yanki wani kaso daga ciki.
Ya ce amma yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zo yana iya ƙoƙarin sa ya ɗauko shugabanni na kirki masu gaskiya da amana ƙarƙashin Alhaji Habu Muhammad Fagge waɗanda basu da tunanin yin wani abu da ba daidai ba ya basu kula da fansho dan haka suna jinjinawa Gwamnan jihar Kano tun zuwansa ya zuba zunzuruntun kuɗi a karon farko yasa Naira biliyan biyar aka biya ya ƙara zuba shida aka biya su yanzu a karo na uku aka ƙara saka biliyan Biyar suka zama Biliyan 16 kenan aka biya ‘yan fansho a tarihin ƙasar nan ba a taɓa samun Gwamna da ya taɓa saka irin wannan kuɗaɗe ba.
Hon. ɗalhatu Bichi ɗan Yalow ya ce da yawa wasu Gwamnoni na tafiya su yi wasu ayyuka saboda wata manufa ko don samun kaso 10 ko don samun wani abu na son kai amma Gwamna Abba saboda kishi da tausayin sa ga al’umma na ƙasa yake ware kuɗaɗen don biyan masu haƙƙoƙin garatuti ga iyalan waɗanda suka rasu da wanɗanda suke a raye domin su yi buƙatun gabansu.