Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya buɗe titin kilomita biyar a garin Dawakin Kudu bayan kammala aikin da ma’aikatar Kula da ayyuka ta jagoranta.
Gwamna Abba Kabir ya ce tun bayan da gwamnatin injiniya Rabi’u musa kwankwaso ta bada aikin titin bayan saukar gwamnatinsa aikin titin ya tsaya a don haka yayi alƙawarin Kamala shi.
Gwamnan ya Kuma gode ma Allah bisa kammala aikin titin Kamar yadda ya ɗauki alƙawarin kammala duk wani titin kilomita biyar a kowace ƙaramar hukumar.
Haka zalika gwamna Abba ya ja hankalin al’ummar ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da su Kula da titin don gudun lalacewa musamman fitulun da akasa don haskakawa.
Taron wanda ya samu halartar kwamishinan ayyuka da gidaje, injiniya Marwan Ahmad,kwamishinan harkokin sufuri Ibrahim Namadi Dala da shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Kudu Hon.Sani Ahmad Mai Rago da masu ruwa da tsaki a jam’iyar NNPP.