Daga RABI’U SANUSI a Kano
Gwamnan Kano,
Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da titi mai tsawon kilomita biyar a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, wanda gwamnatin baya ta yi watsi da aikinsa.
Da ya ke jawabi yayin bude titin, Gwamna Abba ya buƙaci al’ummar yankin da su yi amfani da titin wajen bunƙasa tattalin arziƙinsu.
Ya ce aikin titin na ɗaya ne daga cikin titinan kilomita biyar-biyar da gwamnatin Santa Rabiu Musa Kwankwaso ta fara aiwatarwa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jiha tun a shekarar 2013, wanda ya yi alkawarin kammalawa tun a lokacin yaƙin neman zabensa.
Ya ce titin zai sauƙaƙa al’amuran sufuri da inganta aikin noma da haɓaka tattalin arziƙin al’ummar ƙaramar hukumar.
Ya bayyana rashin Jin daɗinsa bisa yadda gwamnatin da ta gabata tayi watsi da aikin titin duk da alaƙar dake tsakanin gwamnatin wancan lokaci da ƙaramar hukumar.
Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na cigaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da samar wa matasa ayyukan yi da inganta noma da kiwon lafiya da kuma tallafa wa mata da matasa.
Ya kuma ya kira ga al’ummar yankin da su yi amfani da cigaban da gwamnatinsa take kawowa wajen bunƙasa sana’o’insu.
Da ya ke jawabi, Kwamishinan ayyuka na jihar, Alhaji Marwan Ahmad ya ce zuwa yanzu Gwamna Abba ya buɗe titunan kilomita 5 a ƙananan hukumomi Tara inda suma sauran ake daf da kammala su.
Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Abdullahi Magaji Ƙosasshe ya gode wa gwamnan bisa ayyukan raya ƙasa da ya ke aiwatarwa a ƙaramar hukumar tare da yi masa gagarumar kyauta.