Gwamna Abba ya haramta zanga-zanga a faɗin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusif, ta haramta shirya kowane nau’in zanga-zanga a faɗin jihar.

Gwamna Abba ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a safiyar Laraba.

Ya ce, ɗaukar wannan matakin ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu a kan cewa wasu maƙiya jihar sun shirya yin zanga-zangar nuna goyon baya ga Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Hakazalika, Gwamnan ya umarci dukkan hukumomin tsaron jihar da su tabbatar da kama dukkan waɗanda suka samu sun gudanar da zanga-zanga a jihar tare da gurfanar da su a gaban kotu.

A ƙarshe, sanarwar ta ce, Gwamnatin Juhar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.