Gwamna Abba ya kama hanyar naɗa ɗan gidan Kwankwaso muƙamin kwamishina

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf, ya aika da sunan ɗan gidan Rabi’u Kwankwaso, Mustapha Rabi’u Kwankwaso, zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa kafin naɗa shi muƙamin kwamishina a jihar.

Shugaban Manalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar a ranar Talata.

A cewar Falgore, sunayen da Gwamnan ya aike sun haɗa da:

1- Adamu Aliyu Kibiya
2- Usman Shehu Aliyu
3- Mustapha Rabiu Kwankwaso
4- Abduljabbar Garko

Ana sa ran waɗanda lamarin ya shafa su bayyana a gaban Majalisar a ranar Talata, 2 ga watan Afrilun 2024, don a tantance su.