Gwamna Bala ya ƙaddamar da kwamitin farfaɗo da ilimin boko a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed na Bauchi ya danganta faɗuwar darajar ilimi a jihar, musamman ma ilimin firamare ga riƙon sakainar kashi da malaman makarantu suka yi wa koyarwa, haɗi da rashin bibiyar ayyukansu, rashin lura da lamurran koyo da koyarwa na yau da kullum, haɗi da rashin kan gado na malamai.

Ire-iren waɗannan malamai, inji gwamnan, yakan kasance sun karɓi bashin baburan hawa ne domin yin sana’ar acava, da suke biyan waɗannan basussukan a tsintsinke wata-wata, lamarin da ya tilasta masu yin gararambar acava a kowace rana ta duniya, yayin da suka munafirci sana’ar su ta koyarwa.

Gwamnan ya ce: “Abin kunya ne matuƙa gaya a lissafa Bauchi a cikin jihohi ƙasar nan da suke da koma-baya a fannin ilimi, musamman rashin halartar yara a makarantu, duk da cewar gwamnatin mu ta gina ajujuwan karatu kimanin dubu biyar a ‘yan shekaru da suka gabata, amma duk da haka, mun yi tsaikon zaman sojan badakkare, a ƙarƙashin gwamnatoci da suka shuɗe, babu gaba, ballentana baya.

Sanata Bala, ya yi waɗannan tsokaci ne a kwanakin baya yayin ƙaddamar da kwamitin farfaɗo da darajar ilimin boko, wanda ya ƙunshi sarakuna, fitattu da kuma ƙwararrun mutane, musamman kan inganta halartar yara zuwa makarantu, domin magance matsalolin koyo da koyarwa a ɗaukacin makarantun jihar Bauchi.

“Mun shiga cikin wani yanayi, yayin da wani shugaban ƙaramar hukuma, kamar yadda Mai Martaba Sarkin Bauchi ya shaida mana, yana faɗin cewa a ƙaramar hukumarsa, a rubuce akwai malaman makaranta guda 700, amma a zahiri ya ce guda hamsin ne kacal.”

Wasu makarantun ma, basu da malami koda ƙwaya ɗaya. Saboda haka, koda yara sunje makaranta basu da wani abin yi, face wasanni, idan sun gajiya su koma gidajen su”.

Gwamnan ya ƙara da cewa, “wannan mafi munin al’amari ne, kuma wajibi ne a fayyace gaskiya. Dukkan mu muna da laifuka. Wasu daga cikin mu sukan kintata malaman bogi da ake da su a makarantu da zummar maƙare aljifansu da kuɗaɗen albashin waɗannan malaman bogin, suna cin ɓagas, kuma waɗannan mutane masu ci da gumin bogi, sun haɗa har da sarakuna, ‘yan -siyasa, shugabannin ƙananan hukumomi da masu ruwa da tsaki, dadai sauransu, kuma ana samun ire-iren waɗannan halaye tun can baya lokacin da aka ƙirƙiro wannan jiha ta Bauchi.

Sanata Bala Mohammed sai ya buƙaci sarakunan da suka kasance jagororin kwamitin akan ilimi da su ɗauki dukkan matakai nayin gyararraki a dukkan matakan ilimi, tare da matsananci lura kan jami’ai na ilimi a ƙananan hukumomi da hukumar ilimi bai ɗaya ta jiha, haɗi da wasu hukumomi da suke sanya ido a matakan ilimi na firamare, sakandare da gaba da sakandare.

Dangane da haka, sai gwamnan ya zayyana mambobin kwamitin waɗanda suka haɗa da Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu a matsayin shugaba, da kuma sarakunan Katagum, Misau, Jama’are da Ningi da Dass, Alh. Umar Farouk 11, Alh. Ahmed Suleiman, Alh. Nuhu Ahmad Wabi III, Alh. Yunusa Muhammad Ɗanyaya da Alh. Usman Bilyaminu Othman a matsayin mambobin kwamiti.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da shugaban hukumar gudanarwa na makarantun firamare na jiha (SBMC) Kwamishin Ilimi na jiha, Shugaban Hukumar Ilimi bai ɗaya (SUBEB), Babban Sakatare a hukumar BASAME, Shugaban Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) na jiha, Shugaban Asusun Tallafa wa yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF), Shugaban shiyyar Bauchi na hukumar bunƙasa cigaban ƙasa-da-ƙasa (USAID), Shugaban Tawagar Jiha-zuwa-Jiha na USAID, Jami’in Ofishin Kidayar Jama’a na majalisar ɗinkin duniya (UNFP), Shugaban Gidan Talabijin mallakar jiha (BATV), Shugaban Gidan Radiyo na BRC, Shugaban Gidan Radiyo na Globe FM, Jami’in tsare-tsare na ƙungiyar “Plan International, da sauransu, kana babban sakataren a ma’aikatar Ilimi ta jiha a matsayin sakataren kwamiti.

Kwamiti zai haɗa ƙarfi da ƙarfe da hukumomi ma’abuta samar da ilimi ta yadda za a inganta koyarwa wa dukkan yara da ɗalibai, tabbatar da bunkasa lamuran ilimi su kasance kan gaba a dukkan hukumomi gwamnati, haɗi da ƙarfafa fadakar wa akan buƙatar ilimi a dukkan lamurran tafiyar da gwamnati a ɗaukacin jiha baki ɗaya.

Kwamiti, har-ila yau, zai yi bibiya tare da tantance dukkan ayyuka na majiɓantan lamurran makarantu da zummar ana aiwatar da su yadda suka dace da tsarin koyo da koyarwa, haɗi da neman tallafi daga hukumomi da abokan jera tafiya da kungiyoyi ko hukumomi masu zaman kan su, da kuma duk wani lamari da zai taimaka wajen shiga ko daukan yara zuwa makarantu, koyo da koyarwa da kuma samar da ingantaccen ilimi ga yara da dalibai baki ɗaya.

Shugaban kwamitin, kuma mai martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu, a jawabin sa na karban wannan nauyi, a madadin kansa da mambobin kwamiti, ya bayyana gungun ‘yan kwamitin a matsayin wani ladarko da aka ɗora masu nauyin rungumar tafiyar da tsarin ɗaukacin ilimin koyo da koyarwa, yana mai cewar, “kafa wannan ginshikin kwamiti yazo daidai bisa gaɓa na bukatar tallafi damu sarakuna zamu goya wa baya”.

Sarkin ya kuma fahimci cewa lokaci mai tsawo ya shirye da iyayen yara da shugabannin al’umma suka yi kasaɓe suna kallon gwamnati ita kaɗai take bijiro da duk wasu tsare-tsare akan lamurran ilimi, wanda yanzu ta ɗora waɗannan nauye-nauye ko ƙalubaloli akan sarakuna domin kawo tasu gudummawa akan bangaren ilimi.

Mai Martaba Sarkin Rilwanu ya kuma shaidawa Gwamna, “Ina so a madadin ɗaukacin mambobin wannan kwamiti na bayyana farin cikin mu bisa wannan karimci da martabawa da akayi mana na tafiyar da ayyukan wannan kwamiti. Wannan wata dama ce da nauyi da aka ɗora mana da bamu ɗauka da wasa ba”.