Gwamna Bala ya yi wa Buhari wasiƙa a gaggauta kama Sadique ɗan takarar gwamna na APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya aika wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wasiƙa ta musamman yana roƙon shugaban ƙasa da ya gaggauta sawa a kama ɗan takarar gwamnan jihar na APC, Sadique Abubakar bisa zargin wai yana ƙoƙarin tada hankalin jama’a a jihar.

Gwamna Bala ya ce: ”Tunda aka fara kamfen ɗan takarar APC Sadique Abubakar ya ke yin abin da ya ga dama a faɗin jihar. Yana yawo da dakaren jami’an tsaro yana tsorata mutanen jihar.

”Sadiq yana tafiya ne da ayarin jami’an tsaro ɗauke da makamai da ‘yan baranda da aka kawo daga wajen jihar domin ta’addancin ‘yan adawar siyasa da ‘yan jiha da ba su ji ba ba su gani ba. Hakan ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 3 da ba su ji ba ba su gani ba tare da jikkata wasu da dama na qananan hukumomin da ya ziyarta.

“Tawagar Sadique na APC sun haɗa da ‘yan majalisar wakilai biyu Yakubu Dogara da Yakubu Musa Abdullahi, Malam Isah Yuguda, tsohon gwamnan jihar Bauchi, Hon Abdulmumin Kundak, kwamishinan ‘yan sanda, mai ritaya, Bello Illelah, wanda shi ne mai ɗauka da kula da horas da kwamandojin yaƙin ci wa mutane mutunci a jihar.

“Ina so in sanar maka cewa a matsayinsa na tsohon babban hafsan sojojin saman Nijeriya, har yanzu za ka riƙa ganin sa da zaƙaƙumen sojoji da manyan motocin yaƙi suna raka shi duk inda ya nufa.”

A dalilin haka Gwamna Bala, ya yi kira ga Buhari ya sa a kama Sadique a tsare shi.