Gwamna Bello ya hana haƙar ma’adinai a Jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanya dokar dakatar da haƙar ma’adinai a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da kuma Rafi.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Ahmed Ibrahim Matane ya fitar da yammacin Litinin.

Ta cikin sanarwar ‘, sakataren ya ce akwai buƙatar a dakatar da haƙar ma’adinai sakamakon yadda rashin tsaro ke ƙara ƙamari a ‘yan kwanakin nan ta yadda ‘yan bindiga ke kai hare-hare.

Haka kuma ya ƙara da cewa an lura da cewa wuraren haƙar ma’adinai na janyo masu aikata laifuka waɗanda ke ci gaba da zama barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnatin jihar ta Neja, ta kuma yi gargaɗin cewa duk mutanen da aka kama suna haƙar ma’adinai a yankunan da aka sanya dokar za su fuskanci hukunci.

A makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari wata mahaƙar ma’adanai a Jihar Neja, inda suka sace ma’aikata ‘yan ƙasar Chana aƙalla huɗu, tare da kashe jami’an tsaro aƙalla shida Waɗanda suka ƙunshi ‘yan sanda da sojoji da kuma ‘yan sintiri na bijilante a Ƙaramar Hukumar Shiroro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *