Gwamna Bello ya sadar da ɗaliban Islamiyyar Tegina da aka sako da iyayensu

Gwamnatin Jihar Neja ta karɓi ɗaliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina bayan da ‘yan bindiga suka sako su.

Gwamnatin ta karɓi ɗaliban ne a Fadar Gwamnantin Jihar da ke Minna tare da sada su da iyayensu.

Wannan na zuwa kimanin sa’o’i 24 bayan da gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ya dawo daga rangadi na musamman da ya yi kan sha’anin tsaro don ƙarfafa wa rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ke aiki a jihar waɗanda suka yi nasarar fatattakar ‘yan fashin daji daga yankin Mahundu.

Gwamna Abubakar Sani Bello ya yi wa taron manema labarai bayani a gaban yaran da iyayensu da kuma manyan jami’an gwamnati.

Sa’ailin da yake jawabi, Gwamna Bello ya ce baki ɗaya ɗalibai 91 da wasu mutum 2 aka sace inda a yanzu mutum 92 suka kuɓuta sannan guda daga cikin yaran ya rasu.

Daga nan Gwamnan ya yaba wa jami’an tsaro na jihar da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu da Ƙaramar Hukumar Rafi haɗa da dukkan waɗanda suka ba da gudunmawa wajen ceto waɗannan yara.

Gwamnan ya ba da tabbacin cewar za a yaƙi ɓarayin a daƙile su sannan su fuskanci fushin hukuma.

A nasa ɓangaren, shugaban makarantar Islamiyyar, Malam Abubakar Garba Alhassan, ya nuna godiyarsa dangane da irin rawar da gwamnatin jihar da jami’an tsaro da sauran waɗanda suka taimaka suka taka wajen ganin waɗannan yara sun kuɓuta.

Sanarwar da ta fito ta hannun sakatariyar yaɗa labarai ga Gwamna Bello, Mary Noel-Berje, ta nuna yadda iyayen yaran suka yi ta zubar da hawaye saboda murnar ganin ‘ya’yansu bayan shafe kusan watanni uku ba a ga juna ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *