Daga USMAN KAROFI
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa ‘yancin ɓangaren sharia da kuma samar da adalci cikin gaggawa a jihar. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne ranar Litinin, yayin buɗe wani taron horaswa na musamman ga alƙalai, rajistran kotu da ma’aikatan kotu a babban kotun jihar da ke Gusau.
A cewar kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, taron ya bai wa mahalarta damar duba nasarori da ƙalubale a ɓangaren shari’a tare da tsara sabbin hanyoyin da za a bi wajen inganta ayyukan kotu. Gwamnan ya yaba wa shugabar alƙalan jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu saboda shugabancinta na koyi da kuma jajircewarta wajen tabbatar da adalci. Ya ce, “Gwamnati za ta ci gaba da ba da muhimmanci ga shiri da tsare-tsaren da za su kare ‘yancin wannan babban ɓangaren tare da tabbatar da gudanar da shari’a cikin gaggawa.”
Gwamna Lawal ya kuma jaddada muhimmancin amfani da fasaha wajen bunƙasa tsarin shari’a. Ya ce: “Karkatar da tsarin shari’a zuwa na zamani ta hanyar amfani da fasahar zamani zai taimaka wajen rage jinkiri, ƙarfafa gaskiya da tabbatar da adalci cikin sauri.”
Ya kuma yi kira ga ɓangaren shari’a da su kasance masu takatsantsan daga duk wasu mutane da ke ƙoƙarin dagula ayyukan kotu, yana mai cewa “daƙile duk wasu ayyukan cin amana da ka iya lalata martabar ɓangaren shari’a”.