Gwanan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya naɗa sabon Shugaban Hukumomi tare da ɗaukar ƙarin ma’aikata don Sabunta Aikin Raya Birane a jihar.
Naɗin ɓangare ne na matakin Gwamnatin Zamfara ta ɗauka wajen gudanar da ayyukan gina jihar da tara mata kuɗin shiga.
Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Nakwada ne ya sanar da naɗin a Gusau, babban birnin jihar.
Ya ƙara da cewa, naɗin ya haɗa da na sakatarorin hukumar tattara bayanan yanayi ta jihar (ZAGIS) da ta raya birane (ZUREPB).
“Gwamnan ya yi ƙarin naɗe-naɗe na mataimaka don cimma nasara a shirin sabunta aikin raya birane.
“Bugu da ƙari, Gwamnan ya naɗa TPL. Ibrahim Muhammad a matsayin Babban Hadimi na Musamman kan sha’anin tsara gari.
“Sauran waɗanda naɗin ya shafa su ne, Arc. Abdullahi Shehu, Bldr. Jibo Dango, Engr. Bakwai Sa’idu Zurmi, Engr. Abdullahi Bangaje da kuma Q.S Muhammad Sambo Nahuce,” in ji sanarwar.