Gwamna El-Rufai ya shafe awanni a layi domin kaɗa ƙuri’arsa a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shiga jerin gwano domin kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓarsa ta PU024 da ke Unguwan Sarki a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 25 ga watan Febrairu yayin babban zaɓen shugaban ƙasa, El-Rufa’i ya koka da yadda talakawa suka ƙi fitowa kaɗa ƙuri’a a Kaduna, bayan da shafe sama da sa’o’i biyar akan layin kaɗa ƙuri’a a mazaɓarsa, inda ya bayyana damuwarsa kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar.

Da yake jawabi a wata hira da manema labarai a lokacin da yake jiran kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓar PU 024 da ke Unguwan Sarki Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, gwamnan ya yi kira ga jama’a da su fito su kaɗa ƙuri’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *