Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin miƙa mulki mai mambobi 17

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kafa kwamitin miƙa mulki na mambobi 17 ga gwamnati mai jiran gado a jihar.

Majalisar ta kuma amince da wani ƙaramin kwamiti mai mutum 100 wanda za a fitar da Kundin Tsarin Mulkin daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban na jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Malam Muhammad Garba ya sanar da hakan a ranar Lahadi a kano

Ya ce kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Usman Alhaji, yana da mambobi da suka haɗa da Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Babban Lauya/Kwamishanan Shari’a, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamishinan Muhalli da kwamishinan Kasuwanci.

Sauran sun haɗa da Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kudi, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Kwamishinan Ayyuka da Samar da Ababen More Rayuwa, Kwamishinan Kuɗi, Kwamishinan Ilimi da sauransu.

Malam Garba ya bayyana cewa, babban kwamatin zai yi aiki cikin ƙwazo da nufin miƙa mulki cikin makonni uku.

Ya ƙara da cewa an bai wa babban kwamitin na wucin-gadi umarnin fara shirin miƙa mulki tare da rubuta nasarorin da aka samu a cikin wa’adin mulki biyu da aka yi na gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.