Gwamna Ganduje ya miƙa muhimman bayanan gwamnati ga magajinsa

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa mahimman bayanan gwamnati jihar Kano ga gwamna mai jiran gado, Engr Abba Kabir Yusuf, na shekarar 2023.

Wannan ya biyo bayan wani ɗan takaitacciyar ganawa da Ganduje ya samu wakilcin Sakaran Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji, inda ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje yana ƙoƙarin miƙa mulkin cikin kwanciyar hankali a ranar 29 ga watan mayun da ake ciki.

A bayaninsa, gwamnan mai barin gado ya ce yana fatan gwamnati mai zuwa za ta ƙoƙarta wajen duba muhimman bayanan da kundin ya ƙunsa tare da ba su cikakken bayanin abin da suka samu.

Sannan ya kuma miƙa godiyarsa ga mambobin kwamitin miƙa mulki ta yadda suka samar da bayanan har kashi uku da ya shafi jihar baki ɗaya.

A nasa ɓangaren, Gwamna mai jiran gado, Engr Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin Shugaban kwamitin karƙar mulki na jam’iyyar NNPP, Dr Baffa Bichi, ya ce kwamitinsa zai isar da wannan saƙo ga Gwamnan mai jiran gado, tare da bayyana dukkan wani abu da ya kamata idan buƙatar hakan ta taso.

A cewarsa, “A wannan lokacin da ya rage mana saura awanni 105 a miƙa mulkin jihar Kano, haka kuma muna fatan za a yi lafiya kamar yadda al’ummar Jihar Kano ke buƙata a gabatar.”

Wannan bayanin na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran gwamnan mai jiran gado, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar wadda aka raba wa manema labarai, inda ya ce cikakken bayanan za su zama ga al’umma da zarar an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar mai jiran gado da gwamnati mai barin gado sun aminta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *