Gwamna Ganduje ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gaya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Manyan mutane da manyan sarakuna a faɗin ƙasar nan ne suka haɗu a garin Gaya wurin bai wa Sarki Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya (Karmau mai Gabas) sanda, da ya gudana cikin garin Gaya a ranar Asabar da ta gabata.

Sabon sarkin ya gaji mahaifinsa ne Marigayi Alhaji Ibrahim Abdulkadir wanda ya rasu a 22 ga Satumbar shekarar da ta gabata yana da shekara 91.

Naɗin ya biyo bayan amincewar da masu naɗa sarki a fadar suka yi, inda gwamnati ta aminta a naɗa sabon sarkin.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya taya sarkin na Gaya murna, sannan ya roƙi samun zaman lafiya mai ɗorewa ga ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya roƙi sarkin kar ya bari martabar sarautar ta faɗi, ya riƙe girman gidan.

Ya ce gwamnatinsa za ta bayar da cikakken goyon baya ga duk abin da zai ɗaga martabar sarautar.