Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nada Usman Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban ma’aikata na jihar Kano, wanda kafin nadin sa babban sakatare ne a ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar.
Sauran manyan sakatarorin gwamnati da aka naɗa sun hada da, Inginiya Muhammad Bello Shehu, Magaji Lawan, Bilyaminu Gambo Zubairu da Mairo Audi Dambatta.
Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labari na gwamna Abba Anwar ya raba wa manema labarai, yace nadin ya fara aiki ne nan take.
Gwamna Ganduje ya taya su murna sannan ya yaba masu a bisa aiki tuƙuru wajen cigaban al’umma.
Ya ƙara da cewa ” jajircewarku da sanya ƙwarewa a cikin aikinku na yau da kullum ne ya kaiku ga matsayin da aka ba ku. Don haka ku sanya a ranku cewa aiki tuƙuru ne ya sanya kuka maye gurbin waɗansu, don haka lallai idanun mutane na kanku, ku yi ƙoƙari ku bai wa mara da kunya” a cewar gwamna Ganduje.