Gwamna Lawal ya raba tallafin Naira biliyan huɗu ga mutum 44,000 a Zamfara

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon tallafin kuɗi na sama da naira biliyan huɗu ga mutane 44,000 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar. Wannan tallafi wani ɓangare ne na shirin COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus (NG-CARES) da aka gudanar a ɗakin taro na Garba Nadama, JB Yakubu Secretariat, Gusau.

Da yake jawabi a wurin bikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa an tsara shirin don tallafawa masu rauni, inda aka ba mata kaso 60% na kuɗaɗen da aka ware don tabbatar da daidaito da adalci. Ya ce, “Mata zawarawa, waɗanda aka saki da ma’aikatan asibiti masu aikin sadaka sun samu fifiko a wannan shirin.” Ya ƙara da cewa duk da amfani da rajistar tallafi, za a yi amfani da shawarwarin sarakunan gargajiya wajen tantance waɗanda suka cancanta.

A cewar gwamnan, tallafin ya kasu kashi huɗu: “Na farko shi ne shirin Labour-Intensive Public Workfare, inda za a ba kowane mai cin gajiyar shirin N20,000 a kowane wata na tsawon shekara guda. Na biyu shi ne Social Transfers, inda za a ba waɗanda suka kamu da nakasa, tsofaffi da masu fama da cututtuka masu tsanani N10,000 a kowane wata na tsawon shekara guda.”

Haka kuma, Gwamna Lawal ya bayyana cewa za a ba masu sana’o’i ƙanana tallafin N150,000 domin bunƙasa sana’o’insu.

A daya ɓangaren kuma, za a raba tallafin N50,000 ga masu sana’o’i na musamman kamar su ‘yan agaji, mata masu kula da gidajen su kaɗai da kuma ɗalibai na makarantar allo da Islamiya.

A ƙarshe, gwamnan ya yabawa kwamitin gudanarwa na NG-CARES bisa ƙoƙarin su na ganin shirin ya samu nasara. “Wannan nasara ta sanya jiharmu ta sami karramawar musamman daga bankin duniya saboda tsantsar bin tsari da kuma kyakkyawan aiwatar da shirin,” inji shi.